Connect with us

DAGA NA GABA

Koyi Da Kyawawan Dabi’un Fagachin Katsina, Alhaji Iro Mai Kano

Published

on

Shahararren mai ilimin falsafa watau Aristotle ya ce, ‘Nagartattun shuwagabanni su ke yin rige-rige wajen yin abun alheri ga al’ummarsu, su kuma bada gudumuwa ga rayuwar bil’adama ta hanyar bunkasa su da samar masu da nagartaciyyar rayuwa’.

Masarautar Matazu ba wata boyayyiyar masarauta ba ce, ta shahara sosai tun a karni na goma sha hudu. Kodayake, kafin wannan lokacin, wasu malamai masu yada addinin musulunci wadanda ake da yakini ko dai tsatson sahabbai ne, ko kuma dalibai na sahabbai wadanda su ka shigo kasar Hausa don yada addinin musulunci, su suka fara gina garin.

Sun zo, sun yanki wajen zama da kasuwa, sannan su ka gina rijiya, wacce yanzu haka akwai shacin rijiyar da masallacin a wajajen da ake yi wa lakani da shagunan Alhaji Ado kusa da yar-yara a cikin garin Matazu, wannan masallaci kuwa ana masa lakabi da masallacin Kandambara, kafin daga bisani a sauya masa suna ya koma Masallacin Nakandare. Wadannan malamai kuwa, sun zauna a wannan waje a karni na takwas.

Bayan shudewar wani zamani, sai wani Badanaje mai suna Matazu Jabba ya zo, ya sake gina garin Matazu. Da farko ya fara zama a wajen da Sakandaren Jeka-ka-dawo ta garin Matazu ta ke a yanzu wato GDSS Matazu, daga bisani bayan wani bajimin Sa ya gano inda rijiyar Kandambara ta ke, ta hanyar tafiya ya bar ‘yan’uwansa inda yake shiga wani rukuki, ashe wurin rijiya ce da aka gina tsawon zamani, ganin haka sai Matazu Jabba ya tashi ya koma wurin da rijiyar take, wato inda garin Matazu yake a yanzu.

Garin ya samu tagomashin adilan magadai, tun daga Matazu Jabba har zuwa Hakimi na farko a garin wato Fagachin Katsina Hakimin Matazu, Alhaji Iro Maikano. In mu ka yi nazarin wadannan magadai da uwa uba Maigirma Hakimi garin, akwai abubuwan koyi daga rayuwarsu da kuma irin ci gaban da su ka kawo wa masarautarsu da kuma garin Matazu. Wannan ne ya sa garin ya

shahara sosai, ya samu habbakar mutane, yan kasuwa da manoma su ka rika raya garin ta yadda ya bunkasa sosai.

Kasaitar Magadai da Hakimin Matazu ta kai kololuwar yabo ta fanin tsaro, inganta rayuwar talakawa, raya gari, inganta harkokin kasuwanci da noma. Ko lokacin da Sarauniya Amina ta zo kasar Matazu a karni na goma sha shidda (16th Century), ta iske garin zagaye da ganuwa. Wannan ya nuna yadda masu garin su ka ta shi tsaye wajen kawo tsaro a cikin garin Matazu wanda har ya zuwa yanzu akwai wannan kyakyawan tsaro garin. Ko a ‘yan kwanakin nan, Maigirma Fagachin Katsina Hakimin Matazu sai da ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki don inganta tsaro da samar da kakkarfar gidauniyar ilmi ga masarautar da yankin Matazu baki daya.

Tun daga Matazu Jabba har zuwa Fagachin Katsina Hakimin Matazu Alhaji Iro Maikano an samu magadai da dama a garin Matazu, wadannan Magadai da Hakimi sun taka muhimmiyar rawa wajen Kawo ci gaba a cikin al’ummarsu. Kabilun kuwa da suka yi dagacin garin sun hada da; Habe, Fulani, Barebari da Sullubawa. Shi kuwa Fagachin Katsina tsatso ne na Sullubawa wadanda suka taso daga Sokoto, zuriyarsa tsatson Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ce. Fagachin Katsina, Alhaji Iro Maikano mutum ne mai ilimi wanda ke son abinda al’ummarsa ke so.

Yana da sha’awar ya ga matasa na neman ilimi tare da taimakon al’umma da zuriyarsu, yana da sha’awar siyasar gaskiya da rikon amana. Duk sanda ya fito fadarsa, ya kan zauna bisa gadon sarautarsa ya aza kafarsa bisa fatar damisa, sannan ya fara sauraron matsalar al’ummarsa, ba shi komawa cikin gida har sai rana ta fadi.

Haka kuma, ya kasance yana zuwa ziyarorrin zumunci a lokuttan biki ko rasuwa, ko wani ibtila’i in ya faru. Mutum ne mai son neman ilimi, haka kuma yana so ya ga matasa sun tsunduma cikin harkokin ilimi da kimiyya da fasaha da kere-kere da harkokin kasuwanci da noma. Kar mu manta cewa, Fagachin Katsina Hakimin Matazu Alhaji Iro Mai Kano ya yi ilimin Arabiyya da na boko mai zurfi inda ya kware kan ilmin tattalin arziki. Fitaccen mawakin nan Alhaji Aminu Ladan watau Alan Waka ya taba siffanta iliminsa da, “Masani, fakihi, abun alfahari ga kowa, gangaran na Kur’ani…”

Fagachin Katsina, mutum ne mai son ado, haka kuma, sadauki ne wanda baya ja da baya, mun dai ji yadda kakansa Idi Mai Damisa ya shahara a fagen yaki. Shahararren mawakin ya kara hasaso martabarsa inda ya suffanta shi ya ce, “…Barde ka ke mai gwanin sha’awa ga kallo…”.

Fagachin Katsina, Hakimin Matazu Alhaji Iro Mai Kano masani ne a fagen lissafi, a fagen aikinsa lokacin yana aikin gwamnati baya wasa ko kadan. Hubba da zatinsa, da cikar kamalarsa, iliminsa da tattalin al’ummarsa ya taimaka sosai wajen kai garin Matazu kololuwar matakin ci gaba, ta yadda ake kallon garin a cikin jerin kananan hukumomi da suka fi ci gaba a cikin Jihar Katsina. mun karanta daga tarihi yadda Sarkin Musulmi na biyu Muhammadu Bello ya yi wa addini aiki tukuru a shekarar 1817 zuwa 1837, shekaru ashirin na karshen rayuwarsa.

Haka Fagachi ya gaji malamtaka daga kakanninsa wadanda suka jadadda addinin Musulumci a kasar Hausa, ya gaji sadaukantaka wajen Idi Mai Damisa wanda ya ke mayaki kuma amini ga Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, sannan ya gaji harkokin sarauta a wajen kakansa na biyu watau Sarkin Musawa Ibrahim Yero wanda yake siriki kuma amini ga Sarkin Katsina Muhammadu Dikko. Tare da kakansa Sarkin Musawa Ibrahim Yero ne Sarki Dikko ya yi ziyara a Kasar Ingila tare da ibadar aikin Hajji a kasar Saudiyya a shekarar 1921. Kar mu manta cewa, kakansa na daya Matazu Aye yana daga cikin dagatai da su ka rike sarautar garin Matazu.

Bisa wannan ra’in ne suka yi hasashen nazartar rayuwar Fagachin Katsina, domin akwai abubuwan ilmantuwa da ga rayuwarsa da masarautarsa da kuma zuriyarsa. Idan  aka yi la’akari da hakimcinsa, za mu ga cewa rayuwarsa wata baiwa ce da Allah (SWA) ya hallita daban.

Ire-irensu Fagachin Katsina, mutane ne dake da wata baiwa daban da ta sauran al’umma, baiwa irin wacce Allah ya hallitta sannan ya makala irinta gare su.

Kamar yadda su ka yi nazarin Fagachin Katsina, Hakimin Matazu Alhaji Iro Mai Kano, tun yana yaro har zuwa girmansa, Allah (SWA) ya hallice shi mutum ne mai jajircewa, godiya, tausayi, gaskiya da rikon amana, karbar gyara, amincewa da farantawa al’ummarsa, sadaukarwa da sha’awar alkiblar Masarautarsa da al’ummarsa, iya mu’amala da mabambanta al’umma,

tsawatarwa da sassauci, fikirar ma’aunin tunani, yanke saukakkan hukunci, hannun kyauta, karfafa zukatan matasa da kungiyoyi, kirkira da habbaka hanyoyin ci gaba, fuskantar kalubale da samar da hanyoyin warware matsaloli cikin sauri, girmama al’ummarsa, girmama addini da al’ada, iya sarrafa harshe da kuma iya tsara zance cikin hikima, tsoron abinda gobe zata haifar wanda ke sanya shi tashi tsaye don samun mafita kafin goben.

Ire-iren wadannan hakimai suna da hangen nesa da fikirar hasashen abinda gobe zata haifar, sannan su samar da mafita wace zata inganta rayuwar al’ummarsu. Suna da hakurin fuskantar kalubalen al’ummarsu, tare da natsuwa su saurari matsaloli a duk lokacin da wata rashin jituwa ko hatsaniya da ta tashi tsakanin al’ummarsu, su kan natsu don fitar da ingantaccen sakamako ga al’umma. Suna girmama al’ummarsu a kowane yanayi su ka same su tare da tausasar zukatansu in suna cikin kunci ko tsanani, haka kuma su taya su murna ko bakin ciki a duk lokacin da dayan biyun ya samu ga al’ummarsu. Sun aminta a cewa, al’ummar da ke karkashinsu wata ni’ima ce daga cikin ni’imomin da Allah (SWA) ya yi masu, don haka, su kan tausaya masu, su jawo su a jiki, tare da yi masu kyawawan kalamai da sakar masu fuska, haka kuma, su kan daidaitu da matakin al’ummarsu.

(Wannan mukalla Somin tabi ne daga littafin TARIHIN MASARAUTAR MATAZU DA CI GABAN DA TA SAMU wanda Abdulhamid Sani Matazu (Malumman Matazu) Da Bello Hamisu Ida suka rubuta.)

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!