Connect with us

SIYASA

Kano 2019: Takarar Injiniya Abba Kabir An Yi Ne Kan Cancanta —Balaraba Ibrahim

Published

on

An bayyana tsayar da Injiniya Abba Kabir Yusuf da aka yi a matsayin dan takarar Gwamnan Kano a inuwar jam’iyyar PDP da cewa an duba da cewa da cancanta duba da irin gudummuwa gagaruma da ya bayar wajen ci gaban Kano a zamanin mulkin madugun Kwankwasiyya Sanata Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso. Tsohuwar mai bai wa tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso shawara a kan ma’adinai. Hajiya Balaraba Ibrahim ta bayyana haka da take zanta wa da wakilimmu.
Ta ce, a lokacin da dan takarar Gwamnan na Kano yake kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Kano aka sami nasarar yawanci ayyukanda aka yi na manyan titunan kasa dana sama da gadoji da gine-ginen gidajen aman, bandarawo dana Kwankwasiyya da sauran gine-gine na makarantu.
Ta kara da nuni da cewa Abba Kabir jajairtaccene mai yin aiki tukuru da bibiya dukkan ayyukan da ake har sai yaga an kai ga nasara ba kamar yanzu da wannan Gwamnati tazo take abin da taga dama ban a son rai da son azurta kai duk ayyukan da aka dauko na ci gaban Kano da Kwankwaso ya soma an watsar sai lakaki ake a ayyuka da mutane basa ganin anfaninsu.
Hajiya Balaraba Ibrahim ta ce, in Allah ya kawo Abba a matsayin zababben Gwamnan jahar Kano zai zo ya dora ayyuka da za su amfani jama’a da akayi watsi dasu, sannan ya bijiro da wasu fiye ma da wanda aka yi a baya saboda mutumne nagartacce masani a harkar injiniya kuma mai saukin kai da mutunta al’umma da ya kama al’ummar Kano su ba shi goyon baya a zabe mai tunkarowa don kai wa gagacin samar da ci gaba.
Ta kuma ja hankalin yan Kwankwasiyya a kan tun da an fitar da dan takarar Gwamna ya kamata kowa yazo a hada hannu domin ganin jam’iyyar PDP ta sami nasarar kafa Gwamnat a Kano dama kasa baki daya. Domin ko mutum nawane suka nemi takara mutum dayane zai samu, kamar budurwace da manema aurenta za su fito a karshe mutun dayane zai aureta don haka ya kamata azo a marawa Injiniya Abba Kabir baya don samun nasarar.
Hajiya Balara Ibrahim ta ja hanakaln matasa da cewa karsu yarda wani dan siyasa ya basu kwaya dan ya yi anfani da su a zabe mai zuwa su tsaya suyi karatun ta natsu su duba su gani akwai ya, yan wadannan yan siyasa a cikinsu in an fito yakin neman zabe? Duk sun killace ya’yansu suna karatu a kasashe daban-daban su an watsar da su. Wanda a baya zuwan Kwankwaso shi ne yayi kokarin tsamo matasa daga yanda ake anfani da su a bangar siyasa ta killasu da sa su a makarantu ciki da wajen kasar nan da Gwamnatinda ta biyo baya ta watsar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: