Connect with us

MANYAN LABARAI

Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kudurin Samar Da Manyan Makarantu 6

Published

on

Majalisar dattawa ta amine da kudurin da ya bukaci a samar da manyan makarantu shida a yankuna shida na Nijeriya, majalisar ta amince da kudurin ne bayan da shugaban kwamitin majalisar mai kula da al’ammuran manyan makarantu da TETFUND, sanata Barau Jibrin ya shigarwa da majalisar kudurin.

Za a samar da makarantun kimiyya da fasaha guda hudu, kwalejin ilimi guda daya, sai jami’ar kimiyya guda daya, in shugaban kasa ya amince da kudurin za a gina makarantun kimiyyar hudu a garuruwan Mpu dake jihar Inugu, Kwale dake jihar Delta, Kaltungo dake jihar Gombe, sai garin Adikpo dake jihar Benuwai.

Za a gina jami’ar kimiyya ne a garin Auchi na jihar Edo, sannan za a gina kwalejin ilimi a garin Omou-Ekiti na jihar Ekiti, Jibrin ya ce akwai karancin manyan makarantu a kasar nan, don haka yakamata a kara samar da wasu manyan makarantu don a rage wannan rashin, saboda makarantun sune tushen ci gaban kasa.

Sanatan ya ce har yanzu ba a kai ga cimma burin samar da manyan makarantun ba, saboda a cewar shi adadin bai kai kashi 20 daga cikin kashi 100 da ake bukata ba a kasar nan, don haka dole a kara yawan makarantun, sannan a dinga samar da makarantun lokaci bayan lokaci har akai ga cimma wannan adadin.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, sanata Ike Ekweremadu, wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya yabawa sanata Barau Jibrin din, da sauran mambobin kwamitin, saboda kokarin da suka yi na gabatar da wannan kudurin a gaban majalisar, sannan ya bayyana fatan shi a kan wadannan makarantun da irin ci gaban da zasu kawo ma kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!