Connect with us

WASANNI

Real Madrid Na Son Sayar Da Kovacic A Watan Janairu

Published

on

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shirya siyar da dan wasanta, Matteo Kovacic, wanda yake zaman aro a kungiyar Chelsea a watan Janairu mai kamawa.
Kovacic dai yana zaman a kungiyar Chelsea bayan da ya koma kungiyar a watan Agustan da ya gabata sakamakon tsohon kociyan kungiyar ta Real Madrid, Julian Lopeyegui ya bayyana masa cewa ba zai yi amfani dashi ba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Real Madrid za ta nemi Chelsea data biya kudin dan wasan a watan Janairu saboda a cewarta Real Madrid tunda dan wasan yabar kungiyar yake fadin maganganu marasa dadi akan kungiyar.
Har ila yau Real Madrid tana ganin kamar dan wasan baya sha’awar komawa kasar ta Sipaniya da buga wasa saboda kungiyar ta fita daga ransa kuma yanason cigaba da zama a Chelsea nan gaba.
Sai dai abokiyar hamayyar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Tottenham, itama ta nuna tanason siyan dan wasan domin kociyan kungiyar yanason kara karfin tawagarsa musamman a bangaren tsakiya.
Kovacic dai yakoma Real Madrid ne daga kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan a lokacin Rafa Benitez yana kociyan Real Madrid kuma ya buga wasanni 110 a kungiyar sannan ya lashe kofuna da dama.
Har ila yau dan wasan ya je wasan karshe na gasar cin kofin duniya inda ya wakilci kasarsa ta Crotia duk da cewa sunyi rashin nasara a hannun kasar Faransa
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!