Connect with us

RAHOTANNI

’Yan Sanda Na Binciken Jami’an ‘Yan Bangar Da Suka Harbe Matashi A Bauchi

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta kama wasu jami’an kungiyar ‘yan banga masu bayar da tsaro ta Garu Bigilante da suka harbe wani matashi mai suna Abubakar Mahmud Abbati ranar litinin da dare a unguwar rariya da ke Ibo Kuarters a Bauchi.

Kakakkin rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar shi ne ya bayyana haka ga wakilin mu bayan aukuwar lamarin da a halin yanzu kungiyoyin matasa da iyayen yaron dan shekaru 22 suke bayyana korafin su na ganin gwamnatin Jihar Bauchi da hukumomin tsaro sun tabbatar da ganin an hukunta ‘yan kungiyar ta Garu da suka tafka wannan mummunan aiki da nufin suna samar da tsaron jama’a kamar yadda wasu kungiyoyi takwarorin su ke gudanarwa a sassa dabam dabam na kasar nan.

Wakilin mu ya ziyarci unguwar Kurmi inda iyayen matashin ke da zama inda ya tattauna da kakan Abbati mai suna Alhaji Ali Ahmed Danmasanin Ajiya, wanda ya bayyana cewa ya ji labarin kashe yaron ne kamar mafarki, musamman ganin matashin ya shirya ya fita zuwa inda suke aikin dinkin rigunan ‘yan wasa na Magayakin Ajiya, amma lokacin da ‘yan kungiyar ta Garu suka shiga unguwar Rariya da nufin neman matasa ‘yan sara suka amma suka gudu, daga nan sai suka je wannan shago suka duba matasan da ke ciki suke gudanar da ayyukan su na din kayayyaki.

Ya ce bayan isowar su ne sai daya daga matasan ya ce da su bai kamata su rika zuwa shagon su da nufin wai suna neman ‘yan sara suka ba tunda kowa ya san suna aikin neman abin kan su ne don haka bai dace su rika musu barazana da makamai ba. Bayan  sun tafi ne sai wani daga cikin su ya ce su koma su sake samun matasan don hukunta yaron da yayi maganar ya raina musu aiki ne. Isar su ke da wuya sai suka rufe kofar shagon daga nan kuma sai wani daga cikin ‘yan bangar ya koma gefe ya dura harsashi a cikin bindigar sa ya sanya ta cikin wundo yayi ta harbi, inda ya samu matashin ya kashe shi da ‘yan boris sama da goma har suka fasa marar sa, sannan kuma ya raunana wasu mutane biyu daya a hannu daya a kafa.

Don haka Alhaji Ali Ahmed ya ja hankalin gwamnati ta soke lasisin irin wadannan kungiyoyi idan an same su da laifi, saboda ba za su yi abin da ‘yan sanda ke yi ba wajen tsare mutane, idan kuma ba haka ba za a wayi gari mutane su rika neman kare kan su daga ta’addancin irin wadannan kungiyoyi da suke daukar kananan yara ‘yan shaye shaye suna basu bindiga da nufin su yi aikin samar da tsaro. Don haka ya bayyana cewa matukar ba an tashi a tsaye ba za a shiga cikin matsala don kuwa irin wadannan kungiyoyi za su iya zama ana amfani da su wajen aikata ta’addanci ko kuma tawaye a cikin kasa kamar yadda lamarin ya kasance a wasu kasashen Afirka. Don haka ya bukaci gwamnati ta bi musu wannan hakki a fannin shari’a don ganin an hukunta wadanda suka kashe wannan yaro da gangan.

Ita ma mahaifiyar Abubakar mai suna Hauwa Aliyu Ahmed cikin tashin hankali ta bayyana rashin jin dadi na kashe wannan yaro nata da ta bayyana cewa shi kadai ke tallafa mata wajen daukar dawainiyar iyayen sa da kannennsa da ke makaranta da wannan sana’a ta dinki da ya ke yi a shagon Magayakin Ajiya. Saboda mahaifin yaron direba ne da ya jima ba ya aiki saboda rashin lafiya, sauran yara kuma basu girma ba sai shi wannan yaro Abubakar ne ya taso ya kuma gama sakandare yana shirin shiga babbaar makaranta amma dawainiyar gidan su da ke kan sa ke jawo masa cikas har zuwa lokacin da aka kashe shi.

Don haka ta roki gwamnati kan ta bi mata wannan hakki wajen hukunta mutanen da suka kashe mata yaron, kuma ta roki Allah ya saka mata ya bi mata kadi kan wannan kisan gilla da ‘yan kungiyar ta Garu suka yi wa yaron nata. Lamarin da ta kira a zaman cin zarafi da kauce doka da za ta ci gaba da neman Allah ya bi mata kadi don ganin an hukunta dukkan masu hannu a ciki wannan mummunan aiki da aka tafka a kan yaron ta.

Shi ma shugaban kungiyar ta Garu a Jihar Bauchi  Aliyu Ibrahim Yariman Dumi ya bayyana cewa wannan mummunan aiki ya auku ne a lokacin da ya tafi aiki karamar hukumar Alkaleri, sai aka kira shi aka ce mutanen sa sun tafi unguwar Janruwa da ke cikin garin Bauchi inda ‘yan sara suka ja daga amma kuma bayan sun yi fada da su a waccan unguwa sai suka taho unguwar Bakin kura suka shiga Rariya. Daga nan kuma mutanen sa suka bi su cikin unguwar sai aka ce an samu tashin bindiga har wani matashi ya rasa ransa.

Ya ce ba zai tabbatar mutanen sa ne suka yi harbin ko kuma ‘yan sara suka ba tunda maganar na gaban jami’an yan sanda suna bincike kuma har an kama mutanen Garu Security guda 11 wadanda har zuwa yanzu bai yi tozali da su ba. Don haka suna jira ne su ga abin da binciken ‘yan sanda zai bayyana game da wannan lamari. Saboda haka ba zai iya dorasa da wani abu ba kan wannan batun.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar ya tabbarwa wakilin mu cewa rundunar ta kama wasu daga cikin ‘yan kungiyar ta Garu, kuma a halin yanzu suna rike da mutane biyu da ake kyauta zaton sune suka yi wannan harbi, don haka rundunar na ci gaba da bincike kuma duk wanda aka samu da hannu za a gurfanar da shi gaban kotu domin fiskantar hukuncin da ya dace da shi.

Don haka Kamal Datti ya bukaci jama’a su ba rundunar goyon baya game da aikin da take yi, kuma kowa zai gamsu da irin adalcin da za a yi kan wannan batu. Saboda irin wadannan kungiyoyi ana basu dama ne don su taimaka wajen inganta tsaron jama’a ba don su haifar da rudani ko su wuce gona da iri kan aikin da aka dora musu ba. Don haka ko dan sanda ya kashe mutum yana fiskantar hukunci balle kuma dan wata kungiya da aka kafa da nufin tallafawa mutane da jami’an tsaro don a samu zaman lafiya.

Wannan shi ne karo na biyu cikin watanni uku da ake zargin kungiyar ta Garu Security da kashe mutum, saboda a kwanakin baya sun kashe wani matashin mai suna Abubakar a unguwar Kandahar kusa da masallacin Afakallah inda a wancan lokaci ma an kama kusan mutane hudu da suka azabtar da matashin har ya mutu a halin yanzu ana ci gaba da tsare su.

Don haka akwai unguwanni da dama da aka rufe ofisoshin kungiyar saboda zargin su da cin zarafin mutane ko azabtarwa ko kuma kashewa.

Dukkan kokarin da muka yi na tuntubar daraktan kamfanin Garu Security wanda shi ne Ustaz Idris  ya ci tura amma duk lokacin da muka samu zarafin tattaunawa da shi za mu ji ta bakin sa. Haka suma ofishin tsaron farin kaya na Cibil Defence masu yi wa irin wadannan kungiyoyin tsaro rijista wakilin mu na ci gaba da neman jin ta bakin su game da irin ka’idojin da ake bi don kafa wadannanu kngiyoyi da kuma ayyukan da ya kamata ace suna gudanarwa, don tsaron mutane

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!