Connect with us

SIYASA

Babban Abin Da Ya Kawo Mana Masifa A Kasar Nan Shi Ne Canja Mana Kudin Da Aka Yi –Kaftin Umar Abubakar Bakori, (Ritaya)

Published

on

NEBI KAFTIN UMAR ABUBAKAR BAKORI, (ritaya), tsohon Kaftin ne a bataliyan Sojin ruwa ta kasar nan, wanda ya yi ritaya daga aikin na Soja, a halin yanzun kuma yake tafiyar da wasu harkoki na shi na kashin kansa, tare kuma da harkokin siyasa. A wannan tattaunawar da ya yi da LEADERSHIP A YAU, ya yi bita ne a kan hanyoyi da matakan da ya kamata a bi wajen kaucewa duk wata hatsaniya a lokacin babban zabe na 2019 da ke tafe. Ya kuma yi bayani a kan babban abin da ya sanya matsalar cin hanci da rashawa gami da aikata wasu manyan laifuka suka yi kamari a wannan kasar tamu, a karshe kuma ya yi bayani a kan mafita da hanyoyin warware su a bisa masaniyar da yake da ita musamman a kan harkar tsaro. Ya tattauna ne da wakilinmu, Umar A Hunkuyi.

A sha karatu lafiya:

Kaftin a yanzun haka, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bude dandalin kamfen na babban zaben 2019, ‘yan takara da magoya baya duk sun shiga dandali. Wace shawara za ka baiwa ‘yan siyasan kan yanda ya kamata su gudanar da kamfen din na su?

Alhamdulillahi, a shekarar 2014 lokacin zaben 2015, na yi aiki ne a bangaren tsaro, abin da muka lura shi ne, mutane musamman matasa sun san abin da suke so, mafiya yawan matasan da sukan kawo rigima ba su wuce ‘yan shekaru 17 zuwa 27 ba. Wanda kamata ya yi irin su, su kasance ne a daidai wannan lokacin a makarantun gaba da Firamare na kwana, ko kuma suna cikin Jami’o’i, to yaron kuwa da yake a makarantar kwana, ina ya sami lokacin da zai fito ya yi bangar siyasa? Don haka, a lokacin sai muka mayar da hankali a kan irin wadannan matasan. Kuma ni ne shugaban ma’aikata na kungiyar ‘yan sintiri ta kasa, in ka duba zai yi wuya a Jiha a sami masu tayar da rigiman nan guda 5000, to a ce ma ana da dubu 5 din, a Jihar Katsina, muna da rumfunan zabe sama da 5000. Ba ka isa ka ce mani dan tashin hankali guda daya shi ne zai tayar da rigima ba, to tun da matasan a shirye suke suna son a yi zabe na gaskiya, sai suka hada kai da mu, muka wayar masu da kai ta yanda kowa zai kula da Unguwar su, saboda haka, in har mutum guda ya zo ya tayar da rigima, za a fara hayaniya, sai aka lura cewa shi kadai ne, sai a tsame shi kacokam a kaiwa ‘yan sanda, hakan ya sanya a wancan karon aka yi zaben ba tare da wani yamutsi ko tashin hankali ba.

Saboda haka shawarar da zan baiwa  matasa shi ne, su bude idanun su, su dubi masu son tayar da husuma a wuraren su, su sanya ido a kansu. Ina kuma ganin a wannan karon lamurran za su zo mana da sauki, domin an rigaya an fitar da kudin ciyar da jami’an tsaro, a baya, ‘yan siyasa suna ba su kudi, amma a yanzun duk wanda ya amshi kudi daga hannun wani dan siyasa, ba ya karba domin gwamnati ba ta ba su kudi ne ba, kwadayi ne kawai.

To amma, kar a dauka cewa wa matasa su sanya ido a kan masu son tayar da husuma tamkar ce masu ake yi su dauki doka a hannun su?

Dokan kasa ta baiwa kowane dan kasa ‘yancin kare kansa, matasan nan ba cewa aka yi za su shiga yawo ne suna neman masu son tayar da hankali ba, a’a, kowa zai je rumfar zaben sa ne da katin jefa kuri’arsa, ku kun je kada kuri’a, sai kuma ga wani ya zo zai tayar da hankali, to shi mai son tayar da hankalin shi ne za a kama.

 

A wancan zaben na 2015, ka shaida mana kana tare ne da kungiyar ‘yan sintiri ta kasa, har yanzun kana tare da su din ne, kuma a wannan matsayin naka ko ka canza?

Har yanzun ina tare da wannan kungiya ta ‘yan sintiri, a matsayin ‘yan sa kai, kuma ni ne dai shugaban ma’aikata na kungiyar, a yanzun haka kuma mun gabatar da bukatunmu ga Majalisun tarayya, har an yi mashi karatu na 1, na 2, da na 3, a yanzun haka yana gaban shugaban kasa domin ya sanya hannu. Domin ba wata kasa da za ta iya wanzuwa ba tare da hadin kan masu kula da tsaro ‘yan sa kai ba, a kasashen da suka ci gaba abin da ke faruwa kenan, kowa na kallon kowa ne, shi suke kira a turance da, “Nebourhood Watch,” kafin zuwan Turawa a nan arewacin Nijeriya haka muke, ‘yan doka da dogarawa, suke sa ido a kan abin da ke faruwa, duk bako in ya zo an san shi. Amma ‘yan sanda suna Unguwannin Turawa (GRA) ne kadai, su kuwa ‘yan doka da dogarawa suna tare da Sarki ne a cikin Unguwanni. A lokacin, dan doka daya sai ya kama ‘yan ta’adda goma, ya tasa su zuwa duk inda ya kamata, domin an san su, an kuma san gidajen su, in ka ga sun gudu, to sai dai su bar garin, ba kuma za su sake dawowa ba. Amma a yau, mun kai matsayin da ‘yan sanda goma sai dan ta’adda guda ya gagare su kamawa. A halin yanzun irin wannan tsarin na baya ne muke son mu dawo da shi, ta yanda kowa zai kula da inda yake.

Wasu suna alakanta duk rigingimun da ke aukuwa da su kansu ‘yan siyasan ne, a bisa irin kalaman da ‘yan siyasan kansu suke yi a lokutan da suke yakin neman zaben, kamar wadanne irin kalamai ne ya kamata a naka fahimtar ‘yan siyasan su rika yi a wajen yakin neman zaben na su?

Yana da wuya ka ce ma babban mutum ga abin da ya kamata ka fadi, kananan yara ne ya kamata ka ladaftar a kan irin kalaman da ya kamata su rika furtawa, amma babba wanda ya mallaki hankalin kansa, ya ce bai san abin da ya kamata ya furta ba, wannan hukuma ne ya kamata ta hukunta shi. Amma irin yanda suke maganganu ba a hukunta su, shi yake sanya wasu su ma su yi hakan. Amma idan mutum ya fito ya yi maganganun batunci, aka ji shi aka kuma kama shi aka hukunta shi, to wani kuma ba zai yi hakan ba.

Kaftin, ko akwai wasu shawarwari na daban da kake son bayarwa a nan da suka shafi zaman lafiya da ci gaban kasa?

Hakane, maganan da nake son na fada ko shawarar da nake son bayarwa a nan tana da mahimmanci, magana ce da ta shafi tsaro, tsaro a nan ta hanyar dubarbari, ba maganan tsaro ne da ya shafi masu yin harbi ba, a’a, tsaro ne da ya shafi kasuwanci, diflomasiyya, hukumomin gwamnati. Ni ina ganin matukar gwamnatin nan tana son ta sami cikakken iko a kan abin da ya shafi tsaron kasar nan, sai an dubi me ya kawo bunkasar cin hanci da karban rashawa a kasar nan.

Daya daga cikin babban abin da ya kawo mana masifa a wannan tsarin na dimokuradiyya da muke aiki da shi a kasar nan, shi ne yanda aka canza kudin da muke amfani da su, tun daga babbar takardar kudi ta Naira 50, aka kaita har zuwa takardar kudi ta Naira 1000 kwara guda daya tal. Mene ne dalilin da aka yi hakan, shi ne ana kukan, ‘Ghana Must Go,’ (in za ka dauki Naira milyan daya ko biyu, na takardar kudin Naira 20 ko Naira 50, to kana bukatar jakar da ake yi wa lakabi da, ‘Ghana Must Go), amma a yanzun da aka yi kwarar Naira 1000, a aljihun ka sai ka saka Naira milyan guda.

Don haka, ni ina ganin inda gwamnati za ta tsaya ta duba, ta ga yanda za a cire wadannan manyan takardun kudin nan, to ina tabbatar maka da cewa misali, masu kama mutane domin neman kudin fansa, da za su ce a kawo masu milyan 10 misali, to ka fada mani ta inda za a dauki milyan goma a takardun Naira hamsin-hamsin ko Naira ashirin-ashirin, ina za a kai? Matukar muka rage takardun kudin nan manya, zai rage wahalar fitar da kudi masu yawan gaske, in ina son na tura maka kudi milyan guda sai na tura maka kai tsaye daga asusuna na banki, ka ga a nan za a iya sa ido a kai, wane ne mai wannan asusun da ya fitar da kudin, wane ne wancan da ya karbi kudin. Don haka, duk wanda zai nemi kudi a hannun ka, zai yi wuya ya nemi kudi masu yawa domin kudin suna da yawa.

Amma muddin muka bar su a hakan, ko da kuwa an ce ana son su a takardun waje ne na dalar Amurka, mutumin da zai dauki Naira milyan 10 ya je wajen masu canjin kudi yana son a canza ma shi su zuwa dalar ta Amurka, wace irin mota yake bukatar ya dauka da za ta daukar masa wadannan takardun kudin masu yawa haka har na milyan 10? Matukar ba mu cire wadannan manyan takardun kudin ba, ina maka rantsuwa da Allah, maganan tsaro zai yi wahala, mutum zai ce maka ya je ya siyo bindigar AK47 a kan Naira 900,000, in da a ce kananan takardun kudin ne, ta ya zai iya daukan wadannan kudin? ta ya mutum zai iya zama a cikin daji yana yawo da wadannan kudin? amma yanzun abu ne mai sauki, don mutum ya dauki Naira milyan 10 yana yawo da ita a cikin daji abu ne mai sauki.

Amma in an cire wadannan manyan takardun kudaden aka bar kananan, tsanani kar su wuce takardar kudi ta Naira 50. In kana neman takardun kudi na milyan guda a kan takardun Naira hamsin-hamsin, sai ka samu bandir-bandir guda 400, to ka yi tunanin yanda bandir 400 din nan za su kasance, ka ga wannan abu zai kawo kyakkyawan tsaro a kasar nan. Domin yanzun babban inda za a taba mu mu ji zafi shi ne ta hanyar kudi, a aikin Soja, an koyar da mu in kana neman gamawa da mutum shi ne ka dake shi a inda za ka yi ma shi kwaf daya, ba ka yi ta dukan misali hannun sa da kafarsa ba. Amma da zaran ka sami zuciyarsa ka daka shikenan. To yanzun duk juyawan da muke yi a kan kudi ne, to a sanya mikidari a kan kudin, in an yi hakan za a iya rike jama’a, za a iya rike sha’anin tsaro yanda ya kamata, amma in ba hakan aka yi ba, aka tsaya ana cewa, a lura da yanayin shigo da makamai da abin duk da ya yi kama da hakan, duk shirme ne.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!