Connect with us

LABARAI

FOMWAN Da Nisa’us Sunnah Sun Yunkuro Don Kawo Karshen Mace-Macen Aure A Nijeriya

Published

on

A bisa yawaitar mace-macen aure a sakamakon saki da ake yi wa matan musulmai, wata kungiyar addinin Islama mai suna (NISA’US SUNNAH) da hadin guiwar kungiyar mata musulmai ta kasa (FOMWAN) sun yunkuro domin kawo karshen ko rage yawaitar mace-macen auren mata kanana da ake yawan samu a fadin kasar nan ta Nijeriya.
A lokacin kaddamar da shirin don kokarin kawo karshen yaiwatar sake-saken aure a fadin Nijeriya, gamayyar kungiyar Nisa’us Sunnah da Fomwan wanda suka fara kaddamar da shirin a Bauchi da zimmar lalubo bakin zaren matsalar hadi da rage kaifin mace-macen aure a tsakanin jama’a.
Da take jawabinta a wajen taron a Bauchi, Amiriyar Nisa’us Sunnah ta kasa, Hajiya Rabiatu Muhammad Baba ta shaida cewar ‘yan mata da daman gaske an sake su a sakamakon karancin ilimi da rashin ilimin addini da ke addabar jama’a a Arewacin kasar nan.
Amira ta kara da cewa babba kuma mihimmin hanyar shawo kan sakin aure a tsakanin jama’a shine wayar da kan jama’a da ilmantar da su kan zamantakewar aure a tsakanin miji da mata hadi da koyar da su hakkokin da suke rataye a kan kowannensu daidai da yadda addinin Islama ya shimfida.
Ta kuma kara da cewa mafiya yawan iyaye basu koyar da ‘ya’yansu darussan da suka dace gabanin su shiga rayuwa ta aure wanda hakan ke jefa rayuwar ‘ya’yan nasu cikin muhimman hatsari bayan saki.
Hajiya Rabiatu ta bukaci iyaye su yi wa Allah suke baiwa ‘ya’yayensu horon yadda za su zauna a gidan aure lafiya da kuma bin ka’idojin zamantakewa daidai da koyarwar addinin islama domin rage mace-macen aure da ke kara jefa jama’a cikin firgici.
Shugaban kungiyar, ta bayyana cewar Nisa’us Sunnah tana ci gaba da gwagwarmayarta tun shekaru biyu da suka gabata, inda take aiki kafada-kafada wajen taimaka wa rayuwar jama’a da gudanar da aiyukan jin kai. Daga cikin aiyukansu ta ce har da ziyarce-ziyarce zuwa gidan yari domin koyar da fursinoni ilimin da ta dace, shiga gida-gidan jama’a da koyar da su, hadi da zagayawa jiha-jiha domin kokarin kawo karshen mace-macen aure a tsakanin jama’a.
A jawabinta mukaddashiyar shugaban Nisa’us Sunnah ta kasa, Hajiya Khadija Mohammed Auwal ta bukaci mata da ji tsoron Allah su daina kauce wa dokoki da ka’idojin da Alah ya jimshida, ta ce da bukatar matan suke bin umurnin Allah a zamantakewarsu domin rayuwarsu ta inganta.
Ta kuma bukaci bangarorin ma’aurata da a kowani lokaci suke sanya tsoron Allah, soyayya, tausayi da kiyayewa domin zaman aurensu yake inganta, tana mai shaida cewar muddin ana son kawo karshen mace-macen auren dole ne kowa ya rungumi hakuri da kuma afwa hadi da yafiya domin rayuwa take inganta.
Kana ta kuma nemi matan da suke shiga ta kwarai su daina bayyana tsirancinsu hadi da sanya Hijabin da zai rufe musu jiki a kowani waje domin shawo kan matsalar zina a tsakanin jama’a da kuma janyo hankalin da na miji zuwa garesu.
Tun da farko, a jawabinta na maraba, matar gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Khadiza Muhammad Abubakar wacce ta samu wakilci daga matar kwamishinan kudi na jihar Bauchi Hajiya Rukaiya Garba Sarki Akuyam ta nemi kungiyoyin masu zaman kansu da su kara himma domin kawo karshen yawaitar mutuwar aure a tsakanin jama’a, ta nemi kungiyoyin addini suke tsawatarwa da ilmantarwa a kowani lokaci domin zaman aure yake ingantuwa a cikin jama’a.
Da take ganawa da wakilinmu daya daga cikin mambobin kungiyar mata musulmai FOMWAN Hajiya Fatsuma Muhammad ta shaida cewar yawaitar mutuwar aure a tsakanin jama’a na kara jefa al’umma cikin hatsari ta fuskacin janyo alfasha a tsakanin jama’a, ta shaida cewar mace-mace aure na da gayar hatsari don haka ne ta nemi jama’a da kowa ya bayar da tasa gudunmawar domin zaman auren jama’a yake ingantuwa, ta nuna gayar damuwarta kan yadda jama’a suke yawan yin saki a Arewacin kasar nan.
Taron dai wanda ya samu halartar Shugaban kungiyar Nisa’us Sunnah ta kasa Hajiya Aishatu Bichi, da shuganin kungiyar a jahohin Gombe, Yola, Kebbi, Zaria, Kaduna, da kuma jihar Bauchi mai masaukin kadamar da shin kawo karshen mace-macen aure a tsakanin jama’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!