Connect with us

LABARAI

2019: Buhari Ya Kira Taron Gaggawa Na Jam’iyyar APC

Published

on

Majalisar zartaswa ta jam’iyyar APC mai mulki ta shirya ganawar farko da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar (NEC) tun bayan ficewar shugaban majalisar dattajai, Dakta Bukola Saraki daga jam’iyyar.
Kamar yadda wani kusa daga cikin jam’iyyar yake shaida mana, ya ce ganawar musamman din, za ta gudana ne a babban sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja ranar Alhamis da misalin karfe 10 na safe. Ana sa ran za a tattauna kan tsare-tsare da shirye-shiryen jam’iyyar kan zaben 2019 da ke tafe musamman kan zaben fidda gwani na cikin gida.
Ganawar masu ruwa da tsaki na APC din, zai kunshi shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo da zababbun gwamnonin da suke karkashin jam’iyyar tare da shugabanin jam’iyyar ta APC da suke jihohi 36.
Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Kakakin Majalisar wakilai ta Nijeriya, tsofin shugabanin kasa, mataimakan shugaban kasa, wasu tsoffin gwamnoni dukkaninsu mambobin majalisar zastarwa jam’iyyar ne (NEC).
Kwana-kwanan nan ne Bukola Saraki ya fice daga jam’iyyar ta APC, inda ya tsunduma cikin jam’iyyar adawa ta PDP, tare da shi da wasu sanatoci sha biyu, ‘yan majalisar wakilai sha biyu, ‘yan majalisan jahohi, gwamnoni biyu da kuma da wasu mambobin APC da suka fice zuwa PDP.
Jam’iyya mai mulkin ta kuma samu wasu sabbin mambobi cike har da tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Kafin ranar Alhamis ranar gudanar da taron NEC, kafar sadarwa ta Premium Times ta nakalto shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amshi bakwancin wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Billa a ranar Talata da yammaci.
Majiyar daga fadar shugaban kasa ta shaida cewar Mista Buhari zai yi ganawa da masu ruwa da tsaki na APC din ne cikin dare domin tunkarar babban ganawar da za su yi da majalisar zastarwa na jam’iyyar, “Ana tsammanin Shugaban Buhari zai amshi bakwancin Firaminisran Birtaniya, Theresa May, a ranar Labara,”
Majiyar ta kuma shaida cewar, “Da yammacin ranar Laraba zai amshi bakwancin Theresa May, sanan zai halarci taron ganawa na majalisar zastarwa na jam’iyyar APC a ranar Alhamis, sannan kuma zai amshi bakwancin shugaban kasar Jamus, Angela Markel, a ranar Juma’a da safiya,”
Tunin gwamnatin Jamus ta sanar da ganawar shugaba Buhari da Ms Merkel a ranar Juma’ar.
Majiya daga sakatariyar Jam’iyyar APC ta shaida cewar babban makasudin wannan ganawar ita ce domin shirye-shiryen Jam’iyyar dangane da babban zaben 2019 da kuma fitar da jadawalin yadda zaben fidda gwani na jam’iyyar zai wakanu, wanda ake sa ran gudanarwa a watan Satumban da ke tafe. Ana sa ran ganawar NEC zai fitar da ranar gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar wadanda za su wakilci jam’iyyar a zaben 2019 da ke tafe.
A makon da ta gabata ne APC ta zargi hukumar gudanar da zabe ta kasa (INEC) da fitar mata da tsarin zaben fidda gwani daga ita hukumar ta INEC, lamarin da kai tsaye bai yi wa jam’iyyar dadi ba.
APC dai ta yi zargin ne a cikin takardar manema labaru dauke da sanya hanun sakataren yada labarai, Yekini Nabena wanda ya raba a Abuja.
Mr Nabena ya bukaci INEC ta ke tsawa cikin huruminta ba tare da shiga cikin fitar da sirrin jam’iyyar ba.
Jam’iyyar ta shaida cewar tana sane da yadda INEC ta fitar da wasikar da shugabanta Adams Oshiomhole, ya aike mata dangane da zaben fidda gwani na Jam’iyyar domin tunkarar zaben 2019.
“Wannan fitar mana da muhimman tsarinmu da INEC ta yi, ya zo mana da takaici kuma ba zamu lamunci hakan ba,” Inji Mr Nabena.
Kamar yadda tsarin APC din da INEC ta fitar a ranar 17 ga Agustan, yayi nuni da APC ta fitar da ranar 8 ga Satumba a matsayin ranar gudanar da taron jam’iyyar a fadin kasar nan.
A yayin da kuma a ranar 19 ga Satumba APC za ta gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa, zaben fidda gwani na ‘yan majalisun wakilai ta kasa shi zai gudana a ranar 19 ga Satumba, a yayin da kuma zaben fidda gwani na Sanata zai gudana a ranar 20 ga Satumba, na gwamna kuma a ranar 24, inda Kumar fidda gwanin ‘yan majalisun jahohi na jam’iyyar aka tsara gudanar da shi a ranar 29 dukka ga watan Satumba.
Sai dai kuma sanarwar APC wanda Kakakinta Mista Nabena ya fitar ya ce za su canza wadannan ranakun.
Inda ake tsammanin a wannan ganawar da za su yi a ranar Alhamis ne za su fitar da sabon jadawalin zaben fidda gwani na APC domin shirye-shiryen babban zaben 2019 a Nijeriya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: