Wakilinmu" />

2019: Dalilanmu Na Matsa Wa Dankwambo Don Ya Fito Takara –Musa Gambo

Wannan wata hira da muka yi da wani matashin Malami mazaunin garin Zariya, mai kuma magana akan al’amuran yau da kullum, Malam Musa Gambo. A cikin wannan tattaunawa, Malam Musa Gambo, ya bayyana cewa; suna kira ga Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo da ya fito takarar neman Shugabancin kasar nan bisa wasu hujjoji da ya kawo. Ga dai yadda hirar ta wakana.

Za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu?

Sunana Musa Gambo, kuma ni mazaunin cikin garin Zariya ne a Unguwar da ake ce mata Rimin Kambari.

Masu karatu za su so su ji dalilinku da manufarku da suka sa kuke son Dankwambo, Gwamnan Jihar Gombe a yanzu da ya tsaya a matsayin dan takarar Shugaban kasa?

Dalilanmu da ya sa muke son Ibrahim Hassan Dankwambo, Talban Gombe ya fito takarar Shugaban kasa ya kuma zama Shugaban Nijeriya, suna da yawa ba, su misaltuwa. Saboda da ‘yar manuniya ta nuna, Ibrahim Hassan Dankwambo duniya ta sani lallai dan kwarai ne irin albarka. Domin a irin yadda yake tafiyar da jagorancin al’ummar Gombe, kowa ya san a Gwamnonin Nijeriya kaf, ban rage maka ba, ba a yi kamarsa ba a jajircewa.

Yanzu ka ga Ibrahim Hassan Dankwambo a shekara takwas din da zai karasa, wani Gwamnan zai yi shekara goma sha shida bai karasa aikin da Ibrahim Hassan Dankwambo ya yi ba a shekara hudu ba, balle yanzu da zai cika na takwas.

Duk wanda ya san Gombe a shekarun baya, ya shiga Gombe yanzu ya san Gombe za a iya kwatantata da birnin Abuja. Ko babban asibitinsu na Gombe, ba abin da asibitin Abuja zai nuna masa. Jajircewarsa ce ta sa aka gyara, ba don komai ba sai saboda al’ummarsa da talakawan Gombe su mori gwamnati.

Jajircewarsa ta sa lokacin da ake guguwar canji, Allah bai canza shi ba, saboda mutanen Gombe sun nemi zabin alheri a wurin Allah, sai Allah ya nuna musu Ibrahim Hassan Dankwambo shi ne alheri. Kuma sun samu Uwa tagari, sun samu Uba nagari. Kuma idan da za ka lura da kyau har wadansu daga wasu jihohi daban sukan je Gombe su ci abinci saboda kwangilolin gine-gine da hanyoyi da ake yi. Wanda shi kansa Gwamnan, ka turke shi ka ce sai ya fada maka adadin ayyukan da ya yi, ba zai iya misaltuwa ba saboda yawansu.

Yanzu ayyukan da ku ke ganin ya yi a Gombe ne ya sa kuka ce ya kamata ya fito takarar Shugaban kasa?

A cancanta na shekaru yana da shekarun da ya kamata a ce ya zama Shugaban kasa, ba a rika zabo mana tsofaffi ‘yan shekara saba’in da wani abu a ce su jagoranci Nijeriya ba. Ya kamata a ce dan shekara saba’in ya fuskanci Allah ne, ba wai ya ce zai jagoranci mutane ba, domin kwakwalwarsa ta riga ta buba.

Ibrahim Hassan Dankwambo, ka ga ya rike akanta Janaral na kasa gaba daya, wanda ko ya rike akanta Janaral na kasa gaba daya ka ai ko zai iya rike Nijeriya domin ya san sirrin Nijeriya da kambin da za a rike ta. Kuma ya san hanyar da zai bi ya bi da al’ummar Nijeriya dodar, ba hanya mai gargada ba, wanda za su kashe mutane.

Yanzu kuna ganin har cancantar Dankwambo ya kai ga idan ya fito don takarar Shugaban kasa zai iya kayar da Shugaban kasar yanzu, idan har ya yanke shawarar  shi ma zai tsaya?

Ibrahim Hassan Dankwambo ko bai yanke shawarar tsayawa ba, mu mun yanke masa shawarar ya fito ya yi takarar Shugaban kasar nan. Domin lallai idan PDP suka tsayar da shi, mun tabbata za su samu ruwan kuri’u tsululu a wurin al’ummar Nijeriya.

Na farko, ka ga idan da za ka shiga kasashen Yarabawa, Ibrahim Hassan Dankwambo suke yi, haka idan ka shiga kasashen Inyamurai, Ibrahim Hassan Dankwambo suke yi, nan ko shiyyar Arewa shi suke yi, balle ma abin da ya yi shiyyar Gombe ya yi Bauchi. Kai mun yi hira da wasu mutanen Adamawa da wadansu Jihohi makwabtansu suna cewa; lallai Ibrahim Hassan Dankwambo da shi ya zama Gwamnansu da sun wuce haka.

Na farko dai Gombe ba wai ba su da kabilu ba ne suna da shi, amma Ibrahim Hassan Dankwambo bai yarda a take wa kowa hakki ba. Ba rigingimu a jiharsa, sakamakon ya rike Allah yana addu’o’i.

Misali idan wani zai yi aure, za ka ga idan ya samu mata ta gari zuri’ar wane, akan ce gidan wane ne. Akan ce gidan wane, sai ka ji mutum ya ce; gaskiya ni ma kam zan je na auri zuri’ar gidan nan. Lallai ‘yan Gombe sun samu mata ta kwarai, sun kuma samu Uba na kwarai, shi ya sa muke son Ibrahim Hassan Dankwambo ya zo ya ya jagoranci Nijeriya.

Yanzu ke nan kuna ganin idan da PDP za ta tsaida shi a matsayin dan takarar Shugaban kasa , al’ummar Nijeriya za su zabe shi?

‘Yan Nijeriya ma da gudu za su zabi Ibrahim Hassan Dankwambo ko don saboda kashin da suke sha yanzu a kasar nan. Domin za ka ga shi a jiharsa ba rusawa yake yi ba, ginawa yake yi, sabanin wasu jihohi da kuma rusawa suke yi. Ibrahim Hassan Dankwambo ba korar ma’aikata yake yi ba, yana jawo talakawa ne ya saka su a ayyuka, ba kamar yadda wadansu jihohi suke yi ba.

Yanzu ko kwanakin nan Ibrahim Hassan Dankwambo matasa hamsin ya baiwa aiki a Jami’ar Jihar, wanda kuma bayan an ba ka takardar shaidar samun aiki, har kudi za a ba ka ka je ka yi hidima. Fada min, wani Gwamna ne aka samu a kasar nan wanda zai yi hakan? To wanda kuwa yake yi a Jihar Gombe, lallai idan ya samu Nijeriya za a ji dadi fiye da yadda ake tunani.

Idan ka lura da kyau za ka ga Gwamnoni da dama ana cewa babu albashi babu kaza, ba a biyan ‘yan kwangila, ba a biyan ‘yan fansho, amma ko a kwanakin baya Ibrahim Hassan Dankwambo saboda yadda ya dauki ilimi da muhimmanci, Jami’ar Jihar Gombe dukkan kudin da suke bin shi, haka ya tattara ya biya su. Har da ‘yan fensho wadanda suka yi ritaya.

Wanda ko ya san muhimmancin ilimi, ka ga yana bukatar ci gaban duniya ke nan. Wasu a wadansu jihohin ma kashe ilimi suke yi. A wasu jihohi korar Malamai ake yi, amma shi Ibrahim Hassan Dankwambo za ka ga tirenin Malamai yake yi, wanda bai da gogewa sai a kai shi ya goge. Domin bukatuwarsa ba, shi ne ya raba mutum da hanyar cin abincin shi ba har hawan jini ya kashe shi.

Wasu na ganin ai Gombe karamar jiha ce, musamman a Arewa maso Gabas da Arewa baki daya, ya za a yi wanda ya rike karamar Jiha a Arewa ya iya rike kasa kamar Nijeriya mai mutane akalla Miliyan 180?

Ai Ibrahim Hassan Dankwambo ya rike kasar nan, tunda ya rike akanta Janaral, ai ko ya riga ya rike kasar. Kana ina za ka ga akwai wanda akan dauko shi daga karamar kasa ya rike kasa, balle shi ya fito daga babbar kasa. Ashe kuwa Ibrahim Hassan Dankwambo shi ya cancanta ya zama Shugaban kasa a Nijeriya. Domin Gombe a haka ne take aarama, amma a tarihi ba karama ba ce. Kuma Ibrahim Hassan Dankwambo lallai ya wuce a ce ba zai iya rike Nijeriya ba. Domin wanda kuwa ya rike Akanta Janaral kuma har ya sauka ba a samu wata matsala ba, ashe bai zame masa matsala ba.

To wane kira kuke da shi ga ‘yan Nijeriya akan wannan zabin naku?

Kiranmu ga ‘yan Nijeriya shi ne da su fito su rika Ibrahim Hassan Dankwambo ya fito ya jagorance su. Yanzu misali, kamar a nan mu jihar Kaduna, kungiyoyi da dama wadanda shi Ibrahim Hassan Dankwambo, Talban Gombe bai san abin da ake yi ba. A nan jihar Kaduna akwai kungiyoyi da dama na matasa wanda su suna nan suna ta shirye-shirye cewa Ibrahim Hassan Dankwambo suke so. Har ma sun kirkiro wata hula mai suna ‘Dankwambo 2019!’ Wanda shi Dankwambon ma bai san da su ba.

To shi ne soyayya ta gaskiya, ba irin wadansu ba, wadanda kafin su zo sai da aka dunga bin Masallatai ana wa’azi, ana ta yaudarar mutane ana cewa a zabe su, aka bar Allah ana cewa a zabe su su ne za su kawo alheri, za su yi maganin yunwa, ai kuwa da suka zo su ne ma suka kawo yunwar da ta tsananta.

A karshe me za ka ce wanda ba mu tambayeka ba?

To, alhamdu lillahi. Ibrahim Hassan Dankwambo ya fito ya jagoranci al’ummar Nijeriya. Idan ma ya ce ba zai fito ba, to ba ma gidan gwamnati ba, har kofar dakinsa za mu je mu yi zaman dirshan har sai ya amsa mana zai ya fito takarar Shugaban kasar Nijeriya.

 

Exit mobile version