Connect with us

RA'AYINMU

Matsalar Yawaitar Hadurran Kwale-Kwale A Nijeriya

Published

on

Yawaitan hadurran Jiragen ruwa a rafuka da kogunan kasar nan abin damuwa ne matuka. Mutane da yawa suna rasa rayukan su a hadurran na Jiragen ruwa, wanda abin ke ta kara yawaita a kullum, ta yanda mawuyaci ne a kwashe makwanni biyu ba tare da an samu rahoton hadarin Jirgin ruwa ba.

A kwanan nan, akalla yara 19 ne aka bayar da rahoton sun nutse a hadarin Jirgin ruwan a garin Lafiagi, ta karamar hukumar Edu, da ke Jihar Kwara. Jirgin ruwan yana dauke ne da mutane 22, wanda mafiya yawansu duk kananan yara ne, ya nutse ne a lokacin da yake kokarin ketare rafin.

A ranar 12 ga watan Oktoba, dalibai biyar na makarantar, ‘Bictory International School, da ke Angwan Yelwa, ta karamar hukumar Chikun, Jihar Kaduna,’ sun halaka a lokacin da suke kokarin tsallake sashen tashan tura ruwa na Jihar Kaduna, zuwa daya sashen. An alakanta hadarin ne da yi wa Jirgin lodin da ya sha karfin sa.

A ranar 11 ga watan Oktoba, wani Jirgin ya yi hadari a Legas, inda ya ci ran mutum guda, aka kuma iya ceto wasu mutanan 19, tare da raunuka daban-daban a jikkunan su. Jirgin da ya yi hadarin ne a sashen, Oworonshoki, na Third Mainland Bridge, an ce yana kan hanyarsa ne ta zuwa Ikorodu, zuwa CMS.

  Hakanan, a ranar 17 ga watan Satumba, dukkanin fasinjoji 50 sun halaka a wani hadarin Jirgin a Jihar Neja. An alakanta hadarin Jirgin ne da ruwan sama da ya yi ta sauka tamkar da bakin kwarya.

Ba abin mamaki ne ba, yawaitan masu amfani da bin hanyoyin ruwa a matsayin hanyoyin sufurin su, yana daga cikin abin da ke kara yawaitan Jiragen na ruwa. A hukumance, alkalumma sun yi nuni da cewa, Jihohi 22 daga cikin 36 na kasar nan, suna amfani ne da hanyoyin ruwa a matsayin hanyoyin sufurin su. Nijeriya ce ta biyu a matsayin kasar da tafi yawan hanyoyin yin sufuri ta ruwa a duk kasashen Afrika, inda Nijeriya take da hanyoyin ruwa da suka kai nisan kilomita 8, 600.

A cikin dukkanin wadannan hadurran masu ban takaici, babban abu mai jawo hankali shi ne abin da ya shafi rasa rayukan mutane. Babban shugaban hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa, Corporate Serbices, National Inland Waterways Authority (NIWA), Tayo Fadile, ya alakanta yawancin hadurran Jiragen ruwan ne da rashin kula daga sashen masu Jiragen ruwan. Ya ma kara da cewa, wasu Jiragen ruwan sun shafe sama da shekaru 20, sannan kuma masu Jiragen ruwan sun ki su canza masu fasali.

Lissafi ya nuna cewa, yin lodin da ya wuce ka’ida, tukin ganganci, rashin kula, yanayi mara kyau da amfani da kwararrababbun Jiragen. Hakanan su kansu direbobin Jiragen ruwan, neman kudi karfi da yaji, musamman a lokutan bukukuwa, da wasu lokuta na musamman, rashin kwarewar direbobin, da halayyar fasinjojin, yanayi da gazawan Jiragen ruwan, duk suna cikin mahimman abubuwan da ke haddasa hadurran Jiragen ruwan a Nijeriya.

A wasu lokutan, ba a samun isassun rigunan tsira da rai a cikin Jiragen ruwan da ake shakewa da lodi. Kila hakan ne ma ya sanya wasu fasinjojin ba sa sanya Jiragen ruwan a lokutan da suke yin tafiya a cikin Jiragen na ruwa. Don haka, ya kamata kungiyar direbobin Jiragen ruwan ta san cewa yawancin hadurran na Jiragen ruwa, abubuwan da aka lissafo a sama ne suke aukar da su, kuma magance guda a bar sauran ba zai warware mana wannan matsalar ba.

Hukumomin sufuri a duk madafun gwamnati uku da ke duk kasar nan, musamman wadanda suke a yankunan da ake yin tafiye-tafiye a sassan hanyoyin na cikin ruwa, su yi da gaske a kan yanayin da ake tafiye-tafiyen a cikin ruwa, ta hanyar wajabta wa duk masu Jiragen ruwan da a kodawane lokaci, su tabbatar suna bin dokokin da aka kafa a wannan sashen.

Ya kamata a duba lafiyar dukkanin Jiragen da ake yin amfani da su a hanyoyin na cikin ruwa, a yi waje da duk wadanda ba su cancanta ba. A kuma rika gudanar da atisayen sanin makaman aiki ga su direbobin Jiragen ruwan a kai-a kai. Akwai bukatar tabbatar da cancantar su, bai kamata abin ya kasance na, ba ni na iya ba. Inda a yau mutum zai zo, sai a ba shi sitiyarin tuka Jirgin. A kuma rika duba lafiyan Jiragen a kowace shekara da kuma matsayin takardun shaidar cancantar da aka ba su.

Muna kuma yin kira ga duk hukumomin da suke da iko a kan wannan harkan, da su kula da aikin su yanda ya kamata. Ya kamata su rika gudanar da aikin binciken da aka dora masu a kan matuka Jiragen na ruwa;  su kuma rika lura da yanayin da ya dace kafin su saki Jiragen ruwan a cikin ruwayen, su rika kuma lura da dokar da ta hana direbobin Jiragen ruwan kwankwadar barasa, kamar yanda dokar ta haramta wa masu shan giyan kwankwadarta awanni 12 kafin su kama sitiyarin Jiragen ruwan; ya kama masu dubawan su kasance a wurin tun kafin Jiragen su tashi daga tashoshin domin su duba su, hakanan kuma a can inda za su isa, domin tabbatar da cewa ba su kurba ba a kan hanya.

Sannan kuma, da shi ke ana lakanta da yawan hadurran da yin lodin da ya wuce ka’ida ne, to ya kamata a sanya su masu lura da Jiragen ruwan su gudanar da aikin na su yanda ya kamata wajen duba duk wani Jirgin da ya yi lodi kafin ya fanjama a cikin ruwan, a tabbatar da zalaman neman kudi na direbobin bai kai su da dankarawa Jirgin yawan fasinjojin da suka wuce ka’ida din ba.

Muna kuma yin kira ga hukumomi da su bincika tare da gano abubuwan da kan iya lalata Jiragen ruwan domin su fitar da su daga cikin hanyoyin na cikin ruwa.

A namu ra’ayin, wadannan matakan za su taimaka wajen rage hadurran na Jiragen ruwa a cikin kasar mu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!