Connect with us

KASUWANCI

An Bayyana Matsalolin Da Ke Haifar Da Gine-gine Marasa Inganci

Published

on

Shugaban Kungiyar Magina na kasa NIOB Mista Kenneth Nduka ya bayyana cewar,gazwar da masana’antar yin gine-gine take yi a kasar nan ya janyowa tattailin arzikin kasar babban nakasu, inda ya danganta hakan a kan cin hanci da rashawa Acewar Nduka, kokarinbda fannin ya yi a 2018, yaje bayk sosai indan aka kwatanta dana na shekarun da suka gabata duk da dsmar da fannin yake dashi wajen samar da ayyukannyi a kasar nan.Shugaban ya ci gaba da cewa, cin hanci da rashawa ya yiwa fannin dauren demon minti a daukacin fadin kasar nan, inda ya fara tun daga bayar da aikin gini har zuwa kammala aikinnna gini da kuma lura da ginin. A bisa bayanan da hukumar Kididdiga ta kasa NBS ta fitar a 2018 a zangon shekara ta uku a kan tattalin arziki kasar, ya, nuna cewar fannin ya haura da kashi 52.67 bisa dari a zangon shekarar 2018 na uku, inda aka samu karin da ya kai kashi 35.98bisa dari idan aka kwatanta da kashi 16.69 bisa dari da aka samu a duk a cikin kwatar ta 2017. Rahoton ya sanar da cewar, an kuma samu wani karin na kashi 8.59 bisa dari, idan aka kwatanta dana kwatar data gabata. Rahoton ya kara da cewar, a cikin kwatar an kuma samu kashi 16.54 bisa dari. Fannin gine-gine ya bayar da gudunmawar data kai kashi 4.20 bisa dari ga tattalin arzikin kasa a zangon shekarar ta uku ta 2018, inda ya haura sama da kashi 3.13 bisa dari da ya bayar a shekarar data gabata, amma kasa da kashi 5.47 bisa dari na gudunmawar a cikin zango shekara ta biyu ta 2018.
Shugaba Nduka ya bayyana cewar, ya zama wajibi fannin ya kara zagewa wajen bayar da gudunmawar sa a fannin gine-gine, tattalin arzikin kasar da kuma ciyar da kasar gaba. Sai dai ya yi nuni da cewar, abin takaici ne yadda ake samun akasin hakan a fannin a kasar nan. Shugabkn ya kuma nuna takaicin karara a kan yadda ake baiwa wadanda ba yan kasa ba aikin yin kwangilar gini, inda ya ce hakan yana janyo koma baya wajen ciyar da tattalin arzikin kasar gaba. Shugaban wanda ya sanar da hakann ne a hirar da kamfanin dillancin labarai na kasa ya kara da cewa, bincike ya nuna cewar, kashi biyar bisa dari na kacal na aikin gini a kasar nan masu yin gini yan kasar nan suke samu sabanin a wasu kasashen inda suke samun kashi 15 biss dari har su kuma bayar da gudunmawar su ga tattalin arzikin su amma a Nijeriya kashi hudu bisa dari maginan sukrle bayar da tasu gudunmawar a fannin tattalin arzikin kasar nan. Ya yi nuni da cewar, wani abu shi ne mafi yawancin zane-zanen yan Nijeriya ne suke yi ka ba’a sanya su a cikin kula da gine-ginen. Acewar Nduka, duk wani aikin gini da yan kasar waje suka yi a Nijeriya baya taimakwa tattalin arzikin kasar nan. Ya yi nuni cewar, fannin gini na kasar nan yana da wadata da yawa, inda ya buga masali da cewar, idan za’a kashe naira biliyan 10bn a masana’antar, abin zai shafi tattalin arzikinn kasar. Ya bayar da shawarar cewar dokar yin amfani da kayan gida ta man fetur da iskar gas, ya kamata fannin gine-gine shima a sa masa irin ta musamman don kara ciyar da tattalin arzikin kasar nan. A karshe shugaban ya yi kira ga matakan gwamnati uku dake kasar nan suyi dukkan abinda ya dace don rage cin hanci da rashawa a fannin, sanya yan Nijeriya wajen tsare-tsaren gine-gine sannannkuma gwamnati ta kawo wa fannin daukin da ya dace da kuma magance cin hanci da rashawa a fannin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!