Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Sakkwato Ta Baiwa Masu Jinya Naira Miliyan 20.7 A Matsayin Zakka

Published

on

Gwamnatin jihar Sakkawato ta ba da tallafin Naira Miliyan 20.7 ga asibitioci da shagunan siyar da magunguna a fadin jihar a matsayin Zakkah domin tallafawa marasa lafiya. Raba tallafin ya gudana ne a karkashin kulawar Hukumar ba da zakkah da wakafi ta jihar Sakkwaton. Hukumar ta bayyana cewa; wannan tallafi da aka baiwa marasa lafiya, an ba da ne daga Zakkar watanni Uku ne.

Malam Lawal Maidoki, shugaban hukumar, a lokacin ake raba tallafin a Sakkwato, ya bayyana cewa; wannan tallafin an ba da shi domin tallafawa marasa galihu musamman wadanda ba za su iya biyan kudin kula da lafiyarsu ba. Hukumar ta ce shiyasa suka ba da tallafin da ya kai har Naira Miliyan 20.7 ga asibitoci da shagunan siyar da magani, domin tallafawa marasa shi.

Ya kara da cewa; watannin da aka fitar da Zakkar sun hada da; watan Agusta wanda aka ware masa Naira miliyan 6.9  sai Satumba shima aka ware masa Naira miliyan 5.9, sai watan Oktoba da aka ware Naira miliyan  7.9. Ya tabbatar da cewa; gwamnatin jihar zata ci gaba da tallafawa bangaren lafiya domin tabbatar da inganci da walwalar lafiyar jama’ar Sakkwato.

Asibitocin da suka amfana da wadannan tallafi sun hada da; Kware Psychiatric Hospital, Asbitin UDUTH da kuma Specialist Hospital.

Sai sauran sun hada da; Wamakko Orthopedic Hospital, Maryam Abacha Hospital da kuma Iman Hospital. Sai shagunan magunguna sun hada da; Binji Pharmacy, Zumunci Pharmacy, Rauda Pharmacy da kuma Maigobir Pharmacy da sauran su.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!