Connect with us

WASANNI

Man City Sun Ci Mutuncinmu, In Ji Kocin Burton

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Burton, Clough, ya bayyana cewa Manchester City taci mutuncinsu a wasan da suka fafata da ita a ranar Laraba wasan da sukayi rashin nasara daci 9-0
Kafar kungiyar Manchester City daya ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Caraboa Cup, bayan da ta casa kungiyar kwallon kafa ta Burton Albion da ci 9-0 a karawar da suka yi a filin wasa na Ettihad a ranar Laraba.
Manchester City ta ci kwallayen tara ta hannun De Bruyne da Zinchenko da Foden da Walker da Mahrez da Gabriel Jesus wanda ya ci hudu a karawar kuma karo na farko kenan a tarihi da Manchester City taci kwallaye 9 a tarihin kungiyar.
“Duk da cewa basuyi laifi ba kuma wasa ne amma basu mutuntamu ba basu girmama kungiyar muba saboda kwallaye 9 sunyi yawa a ragar kungiyar kwallon kafa kuma mai tarihi kamar kungiyar Burton” in ji kociyan kungiyar
“Yaci gaba da cewa ba wasan kwallon Kwando aka buga ba ko kuma wasan zaru zuga wanda ake cin kwallaye kusan 100 ko sama da haka sai dai yace yana yiwa Manchester City fatan alheri a gasar firimiya
Manchester City za ta ziyarci kungiyar Burton a wasa na biyu a ranar 22 ga watan Janairu yayinda a ranar Talata ne Tottenham ta ci Chelsea daya mai ban haushi a daya wasan daf dana karshen a gasar ta Caraboa Cup ta bana.
Manchester City ce ke rike da kofin Caraboa wanda ta doke Arsenal da ci 3-0 a kakar wasan shekara ta 2017/18 kuma gashi a wannan lokacin ma ta sake zuwa wasan na karshe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!