Connect with us

SIYASA

2019: ’Yan Nijeriya Za Su Mance Da Wahalhalun Rayuwa Idan Su Ka Sake Zaben Mu –Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin cewar muddin ‘yan Nijeriya suka amince da sake zabansa a 2019 zai tabbatar da samar musu da saukin rayuwa, ci gaba da yin aiki tukuru domin Nijeriya ta zama kasa mai wadataccen ci gaba ta fuskoki daban-daban.
Buhari ya yi nuna da cewar zai tabbatar da kyautata rayuwar ‘yan kasa wanda har hakan zai kaisu ga mance wahalhalun da aka fuskanta a baya, domin aiki tukuru da zasu yi muddin suka sake dawowa kan mulki.
Shugaba Buhari wanda ke kawabi a jiya Asabar, a lokacin da suke kaddamar da yakin neman zabem dan takarar gwamnan jihar Bauchi, ya kara da cewa dukkanin alkawuran da ya yi wa ‘yan Nijeriya a 2014 ya samu gagarumar nasarori a kansu, har ma yake cewa zai kuma kara zage damtse wajen yaki da cin hanci da rashawa, shawo kan matsalar tsaro, habaka tattalin arziki da kuma noma.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga jama’an jihar Bauchi da su tabbatar da sun zabi ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben 2019 domin su samu zarafin karasa muhimman aiyukan da suka faru na gina jihar da ma kasa baki daya.
Da yake tasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya nuna cewar muddin jama’an kasar nan suna cike da goyon bayan yaki da rashawa to kada su zabi PDP, a cewarsa APC tana yaki ne da barayi, “Babu wani mutumin kirki da zai kuma so wasu su samu damar ci gaba da cin hanci da rashawa. Don haka mu tabbatar ba mu baiwa masu neman wawushe dukiyar kasar nan daman dalewa kujeru ba. Mu fito mu zabi APC kowa ya zabi APC”, Inji Adams
Adams Oshiomhole, ya daura da cewa, “A bisa abun da muka gani yau a Bauchi mun rigaya ya ma mun yi nasarar lashe zaben 2019. Don haka ina sake jaddada kira a gareku kowa ya tabbatar da zaben dukkanin ‘yan takarar APC a dukkanin matakai daga kasa har sama a yi sak,” A cewar Oshiomhole
Shi kuma a jawabinsa a wajen babban bikin, tsohon gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya nemi yafiyar shugaban kasa Muhammad Buhari ne a bisa abun da ya misalta da ‘kuskuren da aka yi baya’ na kokarin hana yakin neman zaben shugaban kasa na APC a zaben 2014 a cikin filin Sitadiyum na Abubakar Tafawa-Balewa Stadium a lokacin yana gwamnan jihar.
Isa Yuguda ya baiwa Buhari tabbaci da cewa, “Yanzu na dawo cikin APC, zamu yi aiki tare domin tabbatar da nasarar APC a zaben 2019 da ke tafe,” Inji Shi
Shi kuma a nasa fannin, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Babayo Garba Gamawa ya bayar da tabbacinsa na goyon baya dari bisa dari wa shugaban kasa Buhari, yana mai bayanin cewar dukkanin wani dan takarar APC zasu tabbbatar da bashi goyon baya don ganin an hada karfi waje guda domin sake dawo da APC kan mulki.
Shi kuma mai masaukin baki gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya nemi jama’a ne da su yi umumu su fito su zabi ‘yan takarar APC daga sama har kasa domin su samu nasarar cimma muhimman aiyukan da suka faru tun a wa’adin farko.
Gwamnan ya yi amfani da wannan damar wajen kiran jama’an jiharsa da cewa kada su yarda da yaudarar da jam’iyyar adawa ta PDP take zuwa musu da su, ya ce basu da wasu kyawawan manufofi na kyautata rayuwar jama’an jihar.
Ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yaba wa jiga-jigai a siyasar jihar Bauchi da suka dawo cikin jam’iyyar, yana mai bayyana cewar zasu hada karfi da karfe wuri guda domin samun nasarar dawo da shugaban kasa Buhari da gwamna M.A da sauran ‘yan takarar APC a fadin kasar nan.
Darakta Janarar na yakin neman zaben APC Rotimi Amaechi ya shaida cewar a cikin shekaru 3 da APC ta yi a kan mulki ta samu nasarar aiwatar da aiyukan da PDP ta gaza yinsu a tsawon lokacin da ta kwashe tana mulkan kasar nan.
Shi kuma gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar ya nuna irin kyakkyawar shugabancin da kasar nan ta samu a karkashin mulkin Buhari ne, yana mai neman jama’a su sake zaban Buhari domin ya ci gaba da kyautata musu rayuwa. Ya nemi jama’an jihar Bauchi da su yi sak.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!