Connect with us

RA'AYINMU

Bazuwar Makamai Da Kakar Zaben 2019

Published

on

Bincike da kididdiga sun bayyana watsuwar manya-manya da kananun makamai a fadin duniya baki daya, musamman a bangaren da ya shafi ta’addanci da hakan ke sanadiyya rasa rayukan dimbin al’umma da kuma hana gwamnati tafiyar da harkokin mulki kamar yadda ya kamata. Kididdigar ta nuna irin manya-manya da kananan makamai kimanin Milyan 640 da ke bazuwa a duniya a halin yanzu, Milyan 100 na nan a kasashen Afirka. Haka nan kusan Milyan 30 na a jibge ne a Afirka da ke Kudu da Sahara, Milyan takwas kuma a Afirka ta Yamma.

Kusan kaso 59 na yawan wadannan makamai, suna hannun gamagarin mutane, kaso 38 na hannun Sojoji, kaso 2.8 na hannun ‘Yan sanda, sannan kaso 0.2 kuma yana hanun ‘Yan fashi da makami. Idan aka yi wa wadannan bayanai na sama kallon tsanaki, ko shakka babu za a ga cewa, wannan yawaitar makamai da kuma warwatsuwar su, ba karamin abin tsoro ba ne da firgici, musamman a zaben da ke tunkara Nijeriya na 2019. Babban abin tsoron shi ne, yadda ‘Yan ta’adda ke ci gaba da yin safarar manya-manyan makaman suna shigowa da su wannan kasa, ko shakka babu wannan ba karamar barazana ba ce ga zabe mai zuwa.

Har ila yau, yawaita kama makamai da Hukumar hana fasa kwauri (Custom) ke yi shi ya tabbatar da cewa har yanzu ba a dauki hanyar magance matsalar ko hana shigo da manya-manyan makaman ba. Kwana-kwanan nan, Hukumar hana fasa kwauri ta kama irin wadannan makamai da ake zargin an shigo da su daga China inda aka ratso da su daga Kasar Turkiyya zuwa Apapa Jihar Lagas. Haka nan, akwai wani haramtaccen Kamfanin sarrafa muggan makamai da Hukumar ‘Yan sandan farin kaya suka gano a Agbada, Nenwi na Karamar Hukumar Aninri ta Jihar Inugu.

Haka zalika, ‘Yan sandan Nijeriya sun kama kwantena guda 13 dauke da roket-roket da kananan bamabamai na jefawa da hannu da manya-manya da kuma sauran abubuwan fashewa. Masu dauke da wadannan muggan makamai sun bayyana cewa, suna kan hanyarsu ne ta zuwa Gambiya, sun kuma fito ne daga Kasar Iran. Haka nan, an sake samun wani rahoto cewa, jami’an tsaro sun kama wani jirgin Ukrain makile da bindigogi da alburusai a daidai lokacin da jirgin ya sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano. Kazalika, ‘yan watanni kadan da suka gabata, Shugaban Hukumar Kwastan ta Kasa, Col. Hamid Ali, ya bayyana kwace makamai da Hukumar ta yi da yawan su ya kai 1,100 a Jihar Lagas. Sannan a shekarar da ta gabata, an sake kama irin wadannan muggan makamai da su ma yawan su ya kai kusan 2,201, duk da cewa akwai jami’in Hukumar Kwastan din da Hukumar ke tuhuma da zargin hada baki wajen shigowa da makaman. Wadannan da ma wasu abubuwa da ban da ake zargin ‘Yan ta’addan na kokarin yi don ganin an yi kare- jini, biri- jini a zabe mai zuwa na 2019.   

Babban abin takaici shi ne, yadda mafiya yawan wadannan makamai ke hannun ‘Yan ta’adda masu yin garkuwa da mutane da sauran nau’ika na ta’addanci. Irin wannan ta’addanci kamar yin fashi da makami da kuma matsalar makiyaya da ke zargi, sun samu damar cin zarafin al’umma da kuntata musu ta hanyar yin amfani da wadannan muggan makamai. Haka zalika, yawaitar fadan kabilanci da kuma fada tsakanin manoma da makiyaya a Benue, Filato, Taraba da sauran su na daya daga cikin dalilan da suka kawo watsuwar makamai a wannan kasa.

Kasar da ke kan wata gaba ta tunkarar babban zabe mai zuwa, kamata ya yi ta mayar da hankali sosai musamman wajen ci gaba da kwace haramtattun makamai. Kazalika, gwamnati ta ci gaba da hana watsuwar makama a fadin kasar baki daya don tabbatar da ingancen tsaro da zaman lafiya. Sannan ya kamata Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar Majalisar tarayya, su samar da wata doka da za ta hana yaduwar manya da kananun makamai a kowane lungu da sako na wannan kasa. Kazalika ya zama wajibi a dorawa kafatanin jami’an tsaro wannan nauyi, na kawar tare da hana shigo da wadannan makamai daga gungun ‘Yan ta’adda masu son ganin sun haramta zaman lafiya musamman a lokutan da ake fuskanta na zabe.    

Kamar yadda aka sani ne, kasashen da ke safarar irin wadannan makamai, ba a boye suke ba kowa ya san su, tunda mafi yawan su mambobi ne na Kungiyar Kwastan ta duniya. Hadaka tare hadin kai tsakanin wadannan kasashe ne musamman na Hukumar Kwastan, za su iya hana shige da ficen irin wadannan muggan makamai a tsakanin al’umma. Don haka, akwai bukatar sake tantance masu dauke da bindigogi tare da karfafawa wadanda ba su rajista ko lasisi yi cikin wani dan kankanin lokaci, tare da yin amfani da na’urori a guraren shege da fice na jama’a don sake dakile bazuwar wadannan makamai.

A karshe, ya zama wajibi Hukumomin tsaro su sake sanya ido a Bodojin wannan kasa don ci gaba da magance ta’addanci tare da shigo da muggan makamai wadanda ke kara bazarazana ga rayukan ‘Yan Nijeriya da ma kasar baki daya da sauran makamantan su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!