Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mutum Biyar Sun Mutu A Gabzawar ‘Yan Kungiyar Asiri A Asaba

Published

on

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Asaba cikin jihar Delta wannan kuwa ya biyo bayan mutuwar wani mai sayar da Biredi wadanda mutanen da ake sa ran ‘yan kungiyar asiri ne da aikata hakan.
Jaridar SUNDAY PUNCH ta bayyana cewar shi Aboy Sidi an kashe shi ne ranar Alhamis, wajen karfe 6.38 na yamma a sanannan wuri wanda ake kira kwanar Ibusa akan hanyar Nnebisi, an sama shi ne jina-jina.
An dai samu labarin cewar su ‘yan kungiyar asirin wadanda basa ga maciji tsakanin Black Ade da kuma 2-2 Confraternity, wani tashin hankali ne wanda aka fara ranar Asabar ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu, abin dai an fara yin shine ranar Lahadi ta makon daya gabata.
An dai samu labarin cewar ‘yan kungiyar Black Ade dai dai lokacin da ake shirin yin jana’izar ko kuma binne mutumin da aka ce mota ta buge shi ranar Litinin hakan kuma ya su ma wasu , suma sun kai ma’yan wata kungiyar hari ranar Jumma’a.
An dai samu labarin cewar mutane biyu ne inda aka kashe daya sai kuma na daya a Bonssac Umuagwu.
Mutum daya wanda yake mazaunin Asaba wanda ya tattauna da wakilin jaridar Sunday PUNCH, amma bai so a ambaci sunana shi ba, ya bayyana cewar an kashe mutane biyar cikin makon daya gabata an kashe mutum biyar ranar Alhamis, shine kumma na biyar.
“ Na ji labarin cewar sun rufe wani daga ciokin dan’uwan su ranar Jumma’a, kamarcdain yadda nake magana b azan iya sanin abin da zai faru a gaba ba”
Ya ci gaba da bayanin cewar shi wanda ke sayar da biredin an kashe shine lokacin yana a cikin shagon shi, suka zo a akan Keken Napep da wasu mutane hudu,, sai suka fara yin harbi saboda su tsaorata mutanen da suke zama a wurin kafin su bar wurin, kafin su kai ga kashe shi.
Shi dai wannan al’amarin ya faru ne kusa da gidan shi marigayin, wanda hakan ne yaja hankalin shi
Jami’in hulda da jama’a na ‘yansanda Andrew Aniamaka, ya bayyana cewar an ajiye gawar shiu marigayin a dakin ajiye gawa, inda kuma ya ce, za’a ci gaba da yin bincike saboda a gano adanda suke da hannu cikin wajen aikata laifin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: