Connect with us

SIYASA

Rikicin Siyasa Ya Ci Rayukan Mutum Biyu A Kaduna

Published

on

A ranar Litinin da ta gabata ne wadansu matasa biyu suka rasa rayukansu a wani rikici da ya auku a Unguwar Mu’azu, Kaduna.
A cewar shaidu lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin rana. Sun ce matasan, wadanda ake zargin ’yan kungiyar ‘Ba Sulhu’ ne da na ‘Yan Sulhu’ suka fafata a tsakaninsu. Wadannan kungiyoyi biyu matasa ne da suke rikici a tsakaninsu, inda suke kai wa juna hare-hare da miyagun makamai a unguwannin Tudun Wada da Tudun Nufawa da kuma Unguwar Mu’azu.
An ce sun hadu ne a lokacin da ayarin yakin zaben Gwamna Nasir El-Rufa’i ya kai ziyara Unguwar Mu’azu. Sai dai babu bayanin da ya nuna ko rikicin na da alaka da taron siyasa, domin lamarin ya faru ne nesa da inda ake taron a unguwar.
A cewar Baban Khalifa, wanda ya ga yadda abin ya faru, ya ce matasan sun yi amfani da makamai kamar wukake da adduna wajen kai wa juna hari. “Muna inda ake taron siyasa sai kawai daga nesa muka hango mutane na guje-guje, wai matasa na fada. An ce ’yan kungiyar Sulhu ne da Ba Sulhu ke fafatawa.
Kuma akalla mutum biyu ne aka kashe,” inji shi. Wani matashi wanda shi ma abin ya faru a kan idonsa, ya ce daya daga cikin wadanda aka kashe sunansa Salihu kuma makanike ne a unguwar. “Babu ruwansa da kungiyoyin biyu, kawai dai tsautsayi ne ya hau kansa ya ransa,” inji shi. Da Aminiya ta tuntubi Kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo, bai amsa waya ko sakon tes da aka aika masa ba a kan batun.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: