Connect with us

LABARAI

Zabe: Kungiyar CAN Ta Gudanar Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya 

Published

on

Akalla Kiristoci mutum 3,000 ne a jihar Kaduna a jiya Lahadi suka gudanar da wani gangamin addu’a na samun dawwamammen zaman lafiya a zaben da za a gabatar.

Shugaban kungiyar CAN din reshen jihar Kaduna Rabaran John Hayab ya shaidawa manema labarai a Kaduna cewa; sun shirya wannan gangamin addu’ar ne a Cocin Albarka Fellowship Baptist Church dake Television  a Kaduna.

Hayab ya ci gaba da cewa; makasudin shirya gangamin addu’ar shi ne domin rokon Allah da ya kawo mana zaman lafiya a zaben da za a yi mai gabato mu, ya ce; musamman ma idan aka yi la’akari da rashin jituwa da tashin tashina da zaben ke gadarwa, shiyasa suka yi wannan addu’ar domin rokon zaman lafiya. Ya kara da cewa; a matsayinsu na Kiristoci sun yi imani da cewa; ba abin da ya gagari Allah, ya ce; shiyasa ma suka kira Kiristoci da su fito su mika wuya zuwa ga Allah domin neman ganin an yi sahihin zabe cikin kwanciyar hankali.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!