Connect with us

KASASHEN WAJE

Gobara Ta Kashe Mutum 17 A Wani Otel Dake Kasar Indiya

Published

on

Da safiyar yau Talata ne gobara ta kashe mutane 17 a wani Otel dake kasar Indiya. Rahotanni sun nuna cewa; mutanen sun rasa ransu ne sakamakon wannan gobarar da tashi a wani Otel dake unguwar Karol Bagh a Delhi dake kasar Indiya.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce a cikin wadanda suka mutu a gobarar akwai wata mata da yaronta wadanda suka yi kokarin fita ta taga.

Hukumomi a kasar sun bayyana cewa an ceto mutum 35, wasu sun samu raunuka wasu kuma an garzaya da su asibiti. Wasu daga cikin bidiyon da wadanda suka shaida lamarin suka nada a wayoyinsu sun nuna yadda mutane ke tsalle daga ginin Otel din.

Daya daga cikin jami’an kashe gobarar wato Vipin Kenta ya bayyana cewa a yanzu haka an fara gudanar da bincike a kan musabbabin gobarar.

Firaiministan kasar Narendra Modi ya bayyana jimaminsa a kan lamarin a shafinsa na Twitter.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!