Connect with us

Da dimi-diminsa

Hukuncin Kotu: Har Yanzu Babu ‘Yan Takarar APC A Zamfara -Sanata Marafa

Published

on

Dantakarar gwamna a qarqashin jam’iyyar APC, kuma Sanata mai wakoltaw Zamfara ta tsakiya, Sanata Kabir Garba Marafa ya bayyana cewa har yanzu babu ‘yan takarar APC a Jihar Zamfara.

Wannan furuci na Sanata Marafa ya biyo bayan hukuncin da a ke ta yawo da shi na kotun daukaka kara wanda tawagar alqalai uku qarqashin Mai Shari’a Abdul Aboki ta yanke hukunci a jiya Alhamis.

Kotun daukaka karar ta yi watsi da wani hukunci da babbar kotun tarayya ta yi a ranar 25 ga watan Janairun 2015 inda ta goyi bayan INEC kan rashin amsan ‘yan takara daga jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara.

A fashin baqin da ya yi wa Jaridar LEADERSHIP A Yau,  Sanata Kabir Marafa ya ce, “Lallai babu wani abu da ya canza. Tuni lauyoyinmu suna nazarin wannan hukunci domin yau mu turawa INEC matsayarmu. Amma kafin nan, yana da kyau a fahimci cewa kotun daukaka karar ba wai cewa ta yi INEC ta amshi ‘yan takara daga Zamfara ba, a’a wani yanki ne na hukunci aka yi.

“Don haka ina kira ga magoya bayanmu da si kwantar da hankali, duk halin da a ke ciki za mu rika sanar da su, da kuma abin da ya dace su yi a lokutan zabe.” Inji shi
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!