Connect with us

LABARAI

Majalisar Dokokin Jihar Yobe Ta Zabi Mataimakin Kakakin Majalisa

Published

on

Yau da rana ne (Talata) membobin majalisar dokokin jihar Yobe suka zabi Hon. Sa’idu Buba; dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Nangere, a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.

Amincewa da kudurin ayyana sabin mataimakin kakakin, daga Hon. Mohammed Isa Bello, mai wakiltar Mamudo wanda ya samu giyon bayan dan majalisa Ahmed Mirwa daga mazabar Nguru II.

Nada Mista Baba a wannan mukamin ya zo biyo bayan rasuwar tsohon mataimakin kakakin majalisar Dr. Ibrahim Kurmi, wanda Allah ya yiwa cikawa ranar 19 ga watan Fabarairun 2019 a aaibitim koyarwa ta jihar Yobe.

Wanda zaben sa ke da wuya shine akawun majalisar, Ishaku Usman Mohammed ya jagoranci rantsar dashi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!