Connect with us

LABARAI

Kada Ku Yi Wata Harkallar Kudi Da Gwamnati Mai Ci –Zababben Gwamnan Imo Ga Bankuna 

Published

on

Zababben gwamnan jihar Imo, Mista Emeka Ihedioha ya gargadi bankuna da cewa kada su kuskura su yi wata harkallar kudi da gwamnati mai ci, in kuma ba haka ba, za su yiwa kansu, Ihediohan ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da yake wata ganawa da manema labarai yau Alhamis a garin Owerri.

Zababben gwamnan ya ce, daga cikin hakkokin da suka hau kanshi akwai tabbatar da cewa ya hada kan al’ummar jihar gaba dayansu, sannan ya tabbatar da ya hada hannu da al’ummar jihar wajen gudanar da ayyukan da zasu taimaki al’ummar jihar.

A karshe gwamnan ya tabbatar dacewa zai yi iya kokarin shi wajen ganin an tafi da kowa a cikin gwamnatinshi, wacce ya bayyana ta da cewa gwamnati ce ta al’umma, don haka zata yiwa al’umma abinda ya dace.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!