Connect with us

LABARAI

Sufeton ‘Yan Sanda Ya Bukaci Cikakken Bincike A Kan Mutuwar Jami’in NSCDC

Published

on

Shugaban ‘yan sanda na kasa Mohammed Adamu, ya bayar da umurnin gudanar da cikakken binciken mutuwar jami’an hukumar NSCDC, mai suna Ogar Jumbo. Ana zargin cewa, Jumbo ya mutu ne cinkosan ababan hawa a yankin Nyanya da ke Abuja ranar Laraba, lokacin da yake sa’insa da ‘yan sanda. Matar mamacin Ada, tana zargin cewa, ‘yan sanda sun harbe shi inda suka ki kai shi asiti da ruri.
A bayanin shugaban ‘yan sandar na ranar Asabar, ya yi wa iyalan mamacin ta’aziya, tare da hukumar NSCDC, abokai da kuma ‘yan’uwan mamacin, tare da tabbatar musu da cewa za su yi iya bakin kokarin su wajen hukunta wadanda suka aikata wannan mummunar aikin. A bayanin Adamu ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda Frank Mba, ya bayyana cewa hukumar NSCDC tare da iyalan mamacin za su kawo likita domin yin kwacin gawar Jumbo.
Ya ce, “Ba a fara gudanar da gwajin ba, wanda zai tabbatar da musabbabin mutuwar sa, domin taimaka wa bincike. “Bayan haka, shugaban ‘yan sandar ya bukaci iyalan mamacin tare da abokai da kuma daukacin mutane da a kwantar da hankalinsu domin lamarin yana hannun hukuma.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!