Connect with us

RA'AYINMU

Ya Kamata Shugabanni Su Bi Sawun Furayi Minista Ardern

Published

on

Duniya ta yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa Musulman New Zealand a daidai lokacin da suke aiwatar da Sallar Juma’a a masallacin Al Noor da Linwood, a ranar 15 gawatan Mayu, 2019.

Furayi Ministan kasar, Jacinda Ardern, ta bayyana kisan Musulmin su kimanin 50 a matsayin wani mummunan tarihi wanda kasar ba za ta taba mantawa da shi ba. Kazalika a cewarta, tun tale-tale kasar New Zealand, kasa ce da ke baiwa ‘Yan gudun hijira mafaka daga ko’ina a fadin duniya.  Wannan dalili ne ya sa wajibi ne mu ci gaba da baiwa bangaren tsaro muhimmanci don kare rayuka da dukiyoyin kafatanin al’ummar da ke wannan kasa baki daya.

Har ila yau, Furayi Ministan, ta sake bayyana alhini da bakin cinkinta na wannan kisan gilla da aka yi wa masu ibada a masalatai guda biyu a wannan kasa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. Sannan ta aike da sakon ta’aziyya a maimakon ita kanta da kasar New Zealand da kuma gwamnati ga ‘yan’uwan mamatan da sauran daukacin al’ummar kasar baki daya. Ardern, ta kara da cewa, ita da al’ummar New Zealand baki daya, suna kara jajantawa tare da tausawa iyalan wadanda waki’ar ta rutsa da su a wannan ta’addanci da wasu marasa imani da kishin al’umma suka yi.    

“Babu shakka wadannan Shahidai guda 50 da suka rasa rayukansu a wuraren ibada, an yi musu kisa na rashin imani da tausayi. Wurin ibada, wuri ne da ya kamata a ce akwai nutsuwa da walwala, ba wurin da za a biyo mutum a halaka shi ba. Saboda haka, kamar yadda kowa na da ‘yancin yin addinin da ya zaba, wajibi ne kowa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali a wajen gudanar da addinin nasa” in ji Ardern.

Haka zalika, sakamakon firgici da tashin hankali da kasar New Zealand ta samu kanta, ya sa Furayi Ministan ta jagoranci wani tattaki a kasar domin rarrashin wadanda musifar ta’addancin ya shafa kai tsaye da kuma sauran al’ummar kasa baki daya. Ko shakka babu wannan ya nuna irin kulawa tare da sanin makamar aiki da Allah Ya hore wa wannan Shugaba a kan wadanda take jagoranta.

Wakazalika, Furayi Ministan, ta sake yin Allah wadai da wannan mummunan hari, inda a cewarta, ba za taba so ta alakanta kanta da wadanda suka aikata wannan aika-aika ko ta kale su a matsayin halastattun ‘Yan kasar New Zealand ba, saboda irin munin aikin da suka aikata. Sannan ta nemi da cewa lallai a nemo kafatanin sunayen wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan hadari da ya gabata, ba sunayen ‘Yan ta’adda wadanda burinsu bai wuce ganin sun aikata ta’adanci da rashin imani  irin na Shedanu ba.

Ardern, ta yi kira da babbar murya, inda ta ja hankalin ‘Yan kasar da kuma bangaren da ya shafi tsaro a kan yi wa dokar kasar garan bawul wajen mallakar makamai da sauran makamantan su a kasar ta New Zealand. Baya ga yunkurin dakile mallakar makamai a kasar, Furayi Ministan ta sha alwashin taimakawa wadanda suka samu raunuka a farmakin da aka kai masallatan. Haka kuma, ta yi alkawarin daukar nauyin wadanda suka rasa iyalensu da sauran majibantansu a mummunar harin ta hanyar taimaka musu ta hanyoyi daban-daban.

Shugabar New Zealand din, ta bayyana tausayinta irin na Shugabannin kwarai ta hanyar furta kalamai masu kwantar da hankali ga ‘Yan kasar musamman wadanda abin ya shafa. Haka zalika, a yayin da Ardern ta kaiwa iyalan mamatan da sauran wadanda abin ya shafa ziyara ko ta’aziyya, ta je ne sanye da makeken hijabi a kanta don kuntatawa wadanda suka kai wannan mummunar hari da yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 50. Furayi Ministan, ta nuna alhini tare da jajantawa iyalan wadannan mamata, ta kuma bayyana cewa, ko shakka babu wannan darasi ne babba ga kafatanin ‘Yan siyasar duniya baki daya, musamman na Nijeriya ta yadda Shugabanni za su rika daukar matakai a kan ‘Yan ta’adda masu danganta kansu da addini suna cin zarafin ai’ummar kasa.     

Ardern, ta sha alwashin tabbatar da zaman lafiya a New Zealand tare da walwala kamar yadda aka saba. Ta kuma sake yin kira ga sauran ‘Yan siyasa na duniya baki daya da su yi koyi da irin Shugabannin New Zealand. Domin kuwa, a koda yaushe ba su da burin da ya wuce ganin sun fatattaki ta’addanci da ‘Yan ta’adda da ke kokarin labewa a bayan wani addini su ci zarafin wani ko aikata ta’addanci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!