Connect with us

KASUWANCI

Farashin Danyen Mai A Kasuwar Duniya Ya Kara Hawa – Rahoto

Published

on

Farshin danyen mai ya karu tun a cikin watan Numbar shekarar 2018, inda a ranar Litinin data gabata ya kara karuwa saboda yadda kungiyar OPEC take ci gaba da rage farashin sa.
Farahin danyen mai samfarin Brent ya kai dala 70.62 na ko wacce ganga daya a kasuwar duniya da karfe 0716 Agogon GMT a ranar Litinin data gabata, Inda ya kuma tashi zuwa har zuwa kashi 28 ko kashi 0.4 bisa dari a rufewar da ya yo ta karshe a kasuwar.
Danyen mai na kasar Amurka samfarin ( West Tedas Intermediate) ya kai kashi 30 bisa dari ko kashi 0.5 bisa dari akan ko wacce ganga daya ta dala 63.39.
Samfarin danyen mai na Brent WTI faraahin su ya kara karuwa run a cikin watan Nuwamba inda suka kai dala 70.76 da kuma dala 63.48 na ko wacce ganga daya a ranar Litinin data gabata.
Sakamakon karuwar farashin na danyen man a kasuwar ta duniya, kungiyar OPEC da kuma sauran kasashen da ba yayan kungiyar bane kamar kasar Rasha sun ayyana aniyar su ta tura danyen mansu kimanin ganguna miliyan 1.2 a ko wacce rana a cikin wannan shekarar.
Acewar Babban Jami’I samar da dabarun kasuwa na kamfanin FDTM Hussein Saye ci gaba da rage rabar da danyen man da kungiyar ta OPEC keyi da kuma takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasashen Iran da Benezuela hakam ne babban dalilin samun tashin farashkn na danyen man a daukacin wannam shekarar.
Sai dai, karin da aka samu na kwannan ya fati ne saboda da yadda yaki ya kara kazanta a kasar Libiya, inda hakan ya zamo barazana wajen rabar da danyen man.
Rumbun tara bayanan daukar aiki na kasar Amurka a ranar juma’ar data gabata ya nuna crwar, an samu ci gaba a kasuwannin sayar da danyen man ta duniya a rabar Litinin data gabata.
Daraktan a kamfanin makamashi na Energy Consultancy, Trifecta Sukrit Bijayakar ya sanar da cewa, an samu ci gaba a kasuwar.
Ministan Makamashi na kasar Rasha Aledander Nobak a ranar Juma’ar data gabata ya bayyana cewar, kasar sa tana ja da baya wajen shiga yarjejeniya da kungiyar OPEC akan rage yawan danyen man da take sarrafawa, inda mai yuwu wa ta kara sarrafawa yawan danyen man ta in har ba’a kara gusar da yarjejeniyar ba da wa’adinta zai kare a ranar daya ga watan Yuli ba
Yawan danyen man da kasar Rasha take fitarwa ya kai yawan bpd miliyan 11.16 a shekarar data gabata.
Har ila yau, danyen man da kasar Amurka take sarrafawa ya kai yawan bpd miliyan 12.2 a farkon watan Maris kuma danyen man da kasar take fitarwa ya tashi, inda ya kai bpd miliyan uku a karo na farko na wannan shekarar.
A cewar wasu kwararru a fannin makamashi, sakamakon samar da sababbin bututun danyen mai saga watan Yuli, muna sa ran zamu ga habakar bpd 500,000 zuwa bpd 600,000
Bugu da kari, akwai kuma damuwar da ake nunawa akan yanayin tattalin arzikin duniya, musamman ganin cewar, kasashen China da Amurka har yanzu sun gaza kawo karshen rikicin kasuwancin da suka jima suna fafatawa a tsakanin su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!