Connect with us

KASASHEN WAJE

Amurka Ta Ce Za Ta Sake Gina Binuzuwela Idan Suka Tabbatar Da Guaido

Published

on

Amurka ta ce yanzu haka tana aiki tare da wadansu kasashen duniya domin tara dala biliyan 10, wadanda za a yi amfani da su wajen sake gina kasar Benuzuwela matukar dai aka kafa sabuwar gwamnati a kasar.

Sakataren baitulmalin Amurka Steven Mnuchin ne ya sanar da hakan a daidai lokacin da takwaransa na harkokin waje Mike Pompeo ke ganawa da shugabannin kasashen yankin latin Amurka da ke ci gaba da bayyana Juan Guaido a matsayin wanda ke da halascin shugabancin kasar ta Benuzuwela. Mnuchin ya ce, Amurka za ta yi iya kokarinta domin ganin cewa an tara wadannan kudade, kuma tuni Asusun Lamuni na Duniya da kuma Bankin Duniya suka amince da wannan shiri don ceto kasar.

To sai dai a cewarsa, Amurka ba za ta amince wadannan cibiyoyi na kudade sun bayar da tallafi ga Benuzuwela ba har sai zuwa lokacin da aka kafa sabuwar gwamnati da ‘yan kasar suka amince da ita.

Sakataren baitulmalin na Amurka ya ce tabbas jama’ar kasar ta Venezuela na bukatar taimakon gaggawa sakamakon yadda lamurra suka lalace, inda alkaluma ke nuni da cewa adadin ‘yan kasar da suka tsere zuwa ketare saboda rashin iya jagorancin Nicolas Maduro sun kai milyan 3 da dubu 700 a halin yanzu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!