Connect with us

LABARAI

An Yi Kira Da A Bai Wa Mata Muhimmanci A Mukaman Majalisa

Published

on

Wata ‘yar siyasa kuma mai kare hakkin mata mai suna Ann Agom-Eze, ta yi kira da a baiwa mata muhimmanci musamman wajen ba su jagoranci a cikin majalisar kasa ta tara.

Agom-Eze ta yi wannan kiran ne a yau Litinin a garin Abakjaliki. Ta ci gaba da cewa; baya ga shugabancin majalisar Dattawa da na shugaban majalisar wakilai, sauran mukamai ma irin su mataimakin shugaban majalisar dattawa da ta wakilai, da sauran su yana da kyau a baiwa mata mukaman.

Ta tabbatar da cewa; mata suna da dukkanin nagartar da ake son shugaba ya zama da shi wajen shugabanci. Ta ce; idan har aka ba su jagorancin shugabancin majalisar, tabbas za a ga kyakkyawan jagoranci. Ta kara da cewa; idan har ana son wannan majalisar ta tara da ci gaba, wajen bankadowa ‘yan kasa nagartattun ayyukan da za su amfane shi, to tabbas a baiwa mace jagorancin majalisar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!