Connect with us

RAHOTANNI

An Yi Kira Ga Gwamnati Ta Kula Da Yankin Kaura Goje A Kano

Published

on

Daya daga cikin na hannun damar Mataimakin gwamna Dr. Nasiru Yusif gawuna kuma sabon garkuwar ilimin nassarawa, Alhaji Garba Maimaggi singa yayi kira ga gwamnati data kalli yankin Kaura Goje da wasu aikin raya kasa.
Ya yi wannan kira ne lokacin wata gagarumar walima ta samun nasarar gwamna Dr. Abdillahi Umar ganduje a karo na biyu.
Wannan taro ya gudana ne a yankin karamar hukumar nassarawa unguwar PRP da ke mazabar Kaura Goje cikin birnin Kano, taran ya samu halartar manyan yankin musamman yan jamiyyar APC. Yayin wannan taro Garba maimaggi singa yayi kira ga gwamnatin Dr. Abdillahi Umar Ganduje da ta gudanar da wasu ayyuka a yankin, musamman hanyar data taso daga titin gidan ruwa zuwa PRP da kuma inganta asibitin kwararrafa dake unguwar an maida shi babban asibiti.
Domin yankin kaura goje yanki ne mai jamaa matukar gaske, yace irin gudunmawar da wannan yanki na kaura goje yake bayarwa bazata lissafu ba, dalilin bada wannan gudunmawa ya samo asaline saboda irin aiki tsohon chairman din nassarawa Dr. Nasiru Yusif gawuna, ya yiwa wannan yankin wannan yasa Allah ya dubi zuciyarsa ya daukeshi yanzu ya zama mataimakin gwamnan jihar Kano.
Wannan ta sa har yanzu aikinsa bai tsaya ba sai ma fadada aikin yayi zuwa sauran kananan hukumomi, domin ci gaban jihar baki daya. Nasan wannan sabuwar gwamnati da zaa kafa zata kula da sabunta wasu aiyuka da baa yiba.
Wannan yasa muke tuni ko muke rokon gwamnati data dubi wannan kira namu da idan basira, idan akayi wannan hanya to mu yan kaura goje zamu yi farin ciki da gaske domin cigaban nassarawa da mutanen cikinta.
Domin gudunmawar mutanen Kano da suka baiwa wannan gwamnati sun san rasata zai kawo koma baya ga alummar jihar Kano. Wannan tasa suka tashi tsaye wajen kokarin ganin sunyi bakin ko karinsu domin samun nasarar zabe.
Domin akwai wasu ayyuka da gwamna ya faro, to da an samu matsala kwarai domin duk gwamnatin da ta hau to duk aikin da aka fara sunansa an soke shi. To wannan ba karamin koma baya zamu fuskanta ba wannan yasa muke kara kira ga gwamna daya tashi tsaye wajan kirkiro sababbin aiki anan jihar kano.
Da ma duk kananan hukumomin jihar domin irin gudunmawar da gwamnatin nan take samu a yankin kauyuka gaskiya sai muce san barka nasan mataimakin sa Dr. Nasiru Yusif gawuna zai ci gaba da bashi shawara, domin shekara ta 23 gwamnatin mu taci gaba da mulki a wannan jiha.
Domin na san gwamna Allah ya hadashi da jarumi wanda bazai ji kunya ba idan ya gaje shi wajen ci gaba da aiki, dama kowa yasan gawuna maaikaci ne na gaske.
Kai ba shi kadai ba muda muke tare dashi muma muna cin albarkacin sa. gab da kamla taran wata kungiyar da libai ta karraman, Alhaji Garba Maimagi, da kauta ta samun matsayin garkuwar ilimin Nassarawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!