Connect with us

LABARAI

Bikin Easter: Hukumar FRSC Ta Shawarci Matafiya  

Published

on

Sashen Itori na hukumar kiyaye hadurra ta kasa wato FRSC dake jihar Ogun sun shawarci mafiya a motoci da su yi tuki cikin hankali da bin dokokin tuki domin kaucewa fadawa hatsura akan hanya musamman a irin wannan lokacin da wadansu ke tafiya bikin Easter.

Sunday Oko, wanda yake shi ne Kwamandan sashen, shi ne ya ba da wannan shawarar a yayin zantawarsa da manema labarai a garin Ota dake Ogun a yau Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa; mabiya addinin Kirista a duk duniya, za su yi bikin Easter a ranar 19 zuwa 22 ga watan Afrilun shekararnan. Wanda wannan bikin suna yinsa domin tunawa da Yesu Almasihu da kuma fatan tashinsa da za a sake yi.

Oko ya nemi da direbobi da daure su bi dukkanin ka’idojin tuki musamman dokar tuki ta kasa na shekarar 2012, inda ya yi gargadi da cewa; duk wanda aka kama ya karya dokar tukin, to doka za ta yi aiki a kansa. Har wala yau ya shawarci direbobi ‘yan kasuwa da su tabbata da lafiyar motocinsu kafin su dauki mutane zuwa inda za su je domin bikin Easter.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!