Connect with us

RAHOTANNI

’Yan Sanda Sun Kama Wadanda Suka Sace Wakilin Gidan Talabijin Na Channels

Published

on

’Yan sanda sun kama wasu mutane uku da suke da dangantaka da sace wakilin gidan talabijin na Channels, Friday Okeregbe.
‘Yan sandan sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga Kakakin su, Frank Mba, sanarwar ta kara da cewa, a yanzun haka rundunar tana farautar sauran ‘ya’yan kungiyar barayin da suka sace shi din wadanda suka gudu.
Rundunar ‘Yan sandan ta kwatanta wadanda ta Kaman da mutane masu hadarin gaske.
Wadanda ake tuhuman da dukkan su maza ne sun hada da; Hanniel Patrick, 29, dan asalin Jihar Akwa Ibom, Abdulwahab Isah, 28, da Salisu Mohammed 32, dan asalin Jihar Kogi.
A cewar sanarwar ‘Yan sandan, dukkanin su suna bayar da bayanai masu mahimmanci.
Sanarwar ‘yan sandan ta ce, Okeregbe, wanda barayin suka sako shi kwanaki shida da suka gabata, ba shi ne ainihin wanda barayin suka so su sata ba.
“Sai dai, a wannan ranar ta 22 ga watan Maris, 2019, da misalin karfe 07:45, sun sace shi ne a lokacin da suka gan shi yana ajiye motarsa a wani wurin ajiye motoci da ke Lugbe, Abuja. Bincike ya nuna cewa, sun sace shi ne zuwa wata maboyar su da ke Karmo, Abuja.
“’Yan sandan kuma sun gano wata bindiga kirar gida guda daya, harsasan bindigar AK 47 gida uku, Adda, wayoyon hannu da bakaken kyallen da suke rufe fuskar duk wanda suka sata.
Rundunar ta ce, ta himmantu wajen ganin ta kama sauran wakilan tawagar barayin da suka tsere.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!