Connect with us

WASANNI

Ina Son Manchester United Ta Doke City A Satin Gobe – Sir Alex

Published

on

Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Sir Alex Ferguson ya bayyana burinsa na ganin Manchester United tasamu nasara akan Manchester City a wasan hamayyar da za su buga a ranar Laraba mai zuwa.
A ranar Lahadi ne Liverpool ta yi nasarar doke Chelsea da ci 2-0 a wasan mako na 34 a gasar cin kofin firimiyar da suka fafata a filin wasa na Anfield kuma Liverpool ta ci kwallon farko ta hannun Sadio Mane bayan an dawo hutun rabin lokaci, sannan Mohamed Salah ya ci na biyu minti takwas tsakin kwallon Mane.
Da wannan sakamakon Liverpool tana nan a matakinta na daya a kan teburin firimiya da maki 85, ita kuwa Manchester City wadda ta ci Crystal Palace tana ta biyu da maki 83 kuma itama dai Manchester City mai kwantan wasa daya ta doke Crystal Palace 3-1, kuma saura wasanta biyar ya rage a gasar.
“Manchester United ta na bukatar zuwa gasar cin kofin zakarun turai na shekara mai zuwa hakan yana nufin akwai bukatar su samu nasara a dukkan wasanninsu da suka rage musu indai har suna son buga gasar ta turai a shekara mai zuwa” in ji Sir Alex Ferguson
Manchester City tana da wasanni masu zafi da ya hada da karbar bakuncin Tottenham a gasar firimiya da kuma zuwa gidan Manchester United yayinda ita kuwa Liverpool ana ganin wasanninta hudu da suka rage mata ba su da zafi kamar na Manchester City, domin za ta fafata ne da kungiyoyin Cardiff da Huddersfield da Newcastle da kuma Wolbes.
Liverpool za ta ziyarci FC Porto a wasa na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai na Champions League, bayan data ci 2-0 a filin wasanta na Anfield a karawar daf da na kusa da na karshe daga nan ne kuma Liverpool za ta ziyarci Cardiff City a wasan mako na 35 a gasar firimiya ranar 21 ga watan Afirilu.
Kuma a ranar Lahadin dai Jurgen Klopp ya ja ragamar Liverpool wasanni na 200 tun bayan komawarsa Livberpool daga Dortmund kuma a kakar wasan data gabata sunje wasan karshe na kofin zakarun turai sai dai sunyi rashin nasara a hannun Real Madrid daci 3-1.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!