Connect with us

WASANNI

Toni Kroos Zai Iya Barin Real Madrid

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane ya bayyana cewa dan wasan tsakiyar kungiyar, Toni Kroos, zai iya barin kungiyar a karshen wannan kakar da ake bugawa.
Tun farkon wannan shekarar dai ake danganta dan wasan da barin Real Madrid sakamakon kungiyar tayi alkawarin canja dayawa daga cikin ‘yan wasanta kuma tuni aka bayyana cewa yana daya daga cikin ‘yan wasan da zasu iya barin kungiyar.
Zidane yace tabbas akwai ‘yan wasan da zasu bar kungiyar a karshen kaka saboda haka bai san sunayensu ba sai dai yana ganin idan Kroos ya nuna cewa yanason barin kungiyar zasu iya bashi dama domin yatafi.
Sai dai dan wasan a wanann satin ya bayyana cewa bashi da niyyar barin kungiyar kuma duk wani labari da ake yadawa na cewa zai iya barin kungiyar ba gaskiya bane domin bashi da niyyar barin kungiyar.
Wasu jaridu ne dai a kasar Sipaniya suka bayyana cewa dan wasan ya gaji da zaman kasar ta Sipaniya kuma tuni ya roki shugaban kungiyar daya siyar dashi bayan ya shafe kusan shekaru biyar yana bugawa kungiyar wasa.
Toni Kroos ya buga wasanni 35 a wanann kakar sai dai duk da buga wasannin da yakeyi baisa an daina cewa zai bar kungiyar ba kuma ana alakanta dan wasan da komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.
Kroos, dan kasar Jamus ya koma Real Madrid ne daga kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen kuma kawo yanzu ya buga wasanni 228 a kungiyar sannan kuma ya lashe kofin laliga da gasar zakarun turai guda hudu.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ce dai take zawarcin dan wasan tsakiya sakamakon watakila zata iya rabuwa da dan wasa Ander Herrera kuma Toni Kroos ne dan wasan da mai koyar da kungiyar yake ganin zai dace dasu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!