Connect with us

LABARAI

Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Gidajen Malaman Kwalejin Kimiyya Ta Filato

Published

on

Wasu ‘yan bindiga da ba sa san ko su waye ba sun sake kai hari gidajen malaman kwalejin kimiyya a Heifang, karamar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato. Lamarin ya faru ne watanni uku bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidajen malaman tare da sace dan babban limamin cocin makarantar, Rabaran Andrew Dido, kafin daga baya su sako shi bayan biyan kudin fansa.

Rahotanni sun bayyana cewa a wannan karon ‘yan bindigar sun kai harin da dare ne, lokacin da kowa yake bacci inda suka yi awon gaba da ‘yar uwar mataimakin rajistaran makarantar, Ezekiel Rangs.

Rangs wanda ya tabbatar da faruwa lamarin ga manema labarai ranar Litinin da safe ya sanar da cewa suna bacci tare da sauran mutanan gidan wanda ya hada da matar shi, da kanwar shi Abigal ne kwatsam suka ji dirar ‘yan bindigar gidan su da misalin karfe 12:10 na dare

A cewar shi, sun yi amfani da katon dutse wajen balle kofar gidan. Kafin mu ankara ‘yan bindigar sun riga sun shigo cikin gidan. Da muka ga suna dauke da makamai su muka roke su ‘da suyi mana rai’ amma sun yi awon gaba da kanwata wacce ba ta dade da samun gurbin karatu a makarantar ba

Ya kara da cewa, sun nemi mu basu wayar hannu wadda zamu kira su, sai na basu tawa amma sai suka ki karba sai suka karbi ta mata ta sannan suka tafi. Bayan minti 30 da faruwar lamarin wasu soji wanda Konal Tanko yake jagorantan sun zo gidan mu inda na sanar da su abin da ya faru.

Harin da ‘yan bindigar suka kai ba shine karo na farko da suka kai gidajen malaman kwalejin kimiyya Filato ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!