Connect with us

LABARAI

An Yi Kutse A Wayoyin Hannu Ta Hanyar Manhajar WhatsApp

Published

on

A tsakanin jiya Talata da shekaranjiya Litinin, ne aka samu rahoton wani mugun kutse, da wasu da ba a san ko su waye ba suka yi a wayoyin hannu na miliyoyin mutane. Wannan kutsen ya shafi mutane a duk fadin duniya, kuma an yi shi ne ta hanyar manhajar sada zumunta wacce aka fi sani da Whatsapp.

Masu kutsen sun yi amfani da wata fasaha ne, inda suke cusa wata manhaja wacce take satar bayanan sirri a kan wayoyin hannu na mutane, wannan kutsen bai takaita akan wayoyi nau’in Android ba kawai harda wayoyin alfarma na iPhone da ma kwamfutoci.

Zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadin mutanen da kutsen ya shafa ba, masu kutsen suna amfani ne da salon kiran murya da Whatsapp din yake da shi, tamkar dai kiran waya da ake yi, wajen cusa wannan fasahar ta satar bayanan sirri a wayoyin hannun.

Masu bincike suna ganin wani kamfanin kasar Isra’ila mai suna NSO ne ya yi wannan kutsen, an yi wannan kutsen ne da nufin samun damar satar bayanai a wayoyin masu fafutika, lauyoyi da manyan ‘yan jaridu. Ana zargin gwamnatocin wasu kasashe ne su ka siya wannan fasahar ta kutse don satar bayanan sirri daga wajen ‘yan kasa.

Kamfanin Whatsapp din ya yi ikirarin cewa ya shawo kan wannan lamarin, amma an shawarci dukkan masu amfani da manhajar da su sabonta shi wato “Update” saboda kaucewa wannan kutsen da aka yi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!