Connect with us

KASUWANCI

Mutane 20,000 Suka Gabatar Da Takardun Neman Ayyukan Noma A Osun

Published

on

Jiya Talata wani kwatare a fannin aikin noma Mista Isaac Daniels ya sanar da cewar, masana’antar sa ta karbi takardun masu bukatar koyon sarrafa Irin noma a jihar Osun da yawansu ya kai 20,000 da kuma gudanar da wasu ayyukan gona 5,600.

Daniels ya sanar da hakan ne a taron manema labarai da ya kira a garin a garin Osogbo a ranar ta Talata.

Acewar Daniels, gonar tare da hadaka da Ma’aikatar noma ta jihar Osun da kungiyar Manoma ta AFAN da kamfanin Masana’antu da kuma sauran, sun samar da kadada 11,000 don gudanar da aikin.

Acewar Mista Isaac, matasa da dama sun amsa kiran shiga cikin aikin, idan akayi la’akari da dimbin takardun da gonar ta karba, inda hakan ya nuna karara akwai rashin aikin yi a kasar nan mai yawan gaske.

Mista Isaac Daniels ya yi nuni da cewar, idan aka dauki matasan aikin na sarrafa amfanin gona da yin shuka da kuma sauran su hakan zai taimaka wajen rage masu rashin aikin yi a kasar nan.

A karshe Mista Isaac yace, an turwa Bankin ciyar da nahiyar Afirka gaba AfDB don ya bayar da tallafin sa don a fara gudanar da aikin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!