Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Sharhin Da Aka Gabatar A CMG Kan Yakin Ciniki Ya Jawo Hankalin Jama’a

Published

on

A daren Litinin da ya gabata, wani sharhin da aka gabatar kan yakin cinikayyar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a cikin shirin muhimman labarai na gidan telibijin na CCTV na babban rukunin gidajen rediyo da telibijin na kasar Sin wato CMG a takaice ya jawo hankalin jama’a matuka, har masu amfani da yanar gizo sun nuna sha’awa da yabo matuka a kai.

A cikin sharhin, an bayyana cewa, “Game da yakin cinikayyar da Amurka ta tayar da shi, kasar Sin ta riga ta nuna ra’ayinta kamar haka: ba ta son yakin, amma ba ta ji tsoronsa ko kadan, idan har ya zama tilas, za ta mayar da martani, kan matakan da Amurka ta dauka, kasar Sin ta riga ta dauki matakanta, wato idan Amurka tana son yin tattaunawa, to, za ta hada kai, idan Amurka kuma tana son yin yaki, to kasar Sin za ta mayar da martani. Hakika al’ummun kasar Sin sun taba jure wahalhalu iri daban daban a cikin shekaru sama da dubu biyar da suka gabata, ko shakka babu suna iya dakile duk wani kalubalen dake gabansu. Yakin cinikayyar da Amurka ta tayar da shi, wannan wata karamar matsala ce da kasar Sin take fuskanta yayin da take kokarin cimma burin raya kanta, kasar Sin za ta daidaita matsalar yadda ya kamata.”

Sharhin da aka gabatar a cikin shirin, ya kuma nuna wa kasashen duniya ra’ayin kasar Sin kan zaluncin da Amurka ke yi a bangaren cinikayya, wato idan Amurka tana son yin tattaunawa, ita ma kasar Sin tana son yin tattaunawa tare da ita, idan kuma Amurka tana son yin yakin cinikayya, to, kasar Sin za ta mayar da martani nan take, masu amfani da yanar gizo sun bayyana cewa, ra’ayin da kasar Sin ta nuna ya dace da yanayin da kasar ke ciki, suna kuma cike da imani cewa, kasar Sin za ta daidaita matsalar lami lafiya.

Jiya ne kasar Sin ta sanar da cewa, za ta kara sanya haraji kan kayayyakin da kasar Amurka take shiga kasar Sin, a sanadin haka, kasuwar hada-hadar kudin duniya ta gamu da tangarda, rukunin Goldman Sachs wato bankin zuba jari na Amurka shi ma ya fitar da wani rahoto, inda aka nuna cewa, kamfanoni da iyalan Amurkawa ne suka dandanan kudarsu kan matakin kara harajin da Amurka ta yi wa kayayyakin kasar Sin a shekarar bara, kawo yanzu duk da sakamakon da aka samu, hakan na nuna cewa, yakin cinikayya yana kawo illa ga kasashen biyu da ma duniya, yin tattaunawa ita ce hanya daya kacal da ta dace a yi amfani da ita wajen warware wannan matsala, kana gudanar da hadin gwiwa ita ce mafita daya tilo da ta dace a gabanmu.

(Jamila)
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!