Connect with us

Nahiyar Afirka

Gwamnatin Nijar Ta Umurci Zaman Makokin Kwana Uku Kan Sojojinta Da Aka Kashe

Published

on

Gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta ware kwanaki uku daga yau Alhamis domin alhini da makokin mutuwar sojojin kasar 28 sakamakon harin ta’addaanci da aka kai ranar Talatar da ta gabata.

Da farko dai majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojoji 17 ne suka rasa rayukansu yayin da 11 suka bata, to amma daga bisani an bayyana su ma sun rasa rayukansu a wannan hari da ya faru a Baley Beri kusa da iyakar kasar da Mali.

Motoci 8 na bataliyar sojojin kundumbala mai 112 da ke da babbar cibiyarsu a garin Walam ne aka kai wa wannan hari na kwanton bauna, a wani wuri mai tazarar kilomita 45 a arewacin garin Mangaize, kusa da kauyen Tongo-Tongo gaf da iyakar kasar ta Nijar da Mali. Rahotanni sun tabbatar da cewa; a jimilce sojoji 52 ne ke cikin wannan ayari da ke kokarin murkushe ‘yan ta’addar da suka kai hari a gidan yarin Kuti-Kale, inda daya daga cikin motocin sojin ta taka nakiya.

Bayan fashewar nakiyar, nan take ‘yan ta’addar suka bude wa sojojin wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar 17 daga cikinsu, daya ya samu rauni yayin da har yanzu ake ci gaba da neman wasu 11. Rahotanni sun ce jim kadan bayan faruwar harin, an ga jiragen yaki guda uku, daya na Nijar, daya na Faransa da kuma daya na Amurka na shawagi a kusa da inda lamarin ya faru, to sai dai wasu majiyoyi sun ce wadannan jirage sun dawo sansaninsu da ke Yamai ba tare da sun yi nasarar kama ko da daya daga cikin ‘yan ta’addar ba.

Ga alama dai ba daya daga cikin wadannan ‘yan ta’adda da ya tsallaka iyakar kasar ta Nijar zuwa Mali, yayin da wata majiya ke cewa sun samu mafaka ne a cikin al’ummar da ke rayuwa a kauyukan da ke wannan yanki.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!