Connect with us

LABARAI

Nasarar Buhari Daga Allah Ne-Oba Na Legas

Published

on

Oba na Legas, Oba Rilwan Akiolu ya bayyana cewa nasarar da Buhari ya samu na sake zama shugaban kasa a karo na biyu ya nuna cewa Allah ne yake ba da mulki ba wani ba. Oba Rilwan Akiolu ya bayyana hakan ne a yayin da wata tawaga daga makarantar NIPSS, Kuru ta kai masa a fadarsa da ke Legas.

Masu ziyarar wadanda suka kai a karkashin mukaddashin daraktan makarantar, Dk. Nasiruddeen Usman. Rahotanni sun tabbatar da cewa masu ziyarar sun je jihar Legas ne a wani ziyarar gani da ido da suke yi a jihar.

Akiolu ya ce; shugaban kasa ya samu nasararsa a karo na biyu a wurin Allah ta hannun ‘yan Nijeriya. Ya ce; zancen tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo kafin zabe cewa Buhari ba zai ci zabe ba saboda ba ya goyon bayansa, ya zama zancen kawai.

Akiolu ya ce Obasanjo a koyaushe sai ya rika nuna yana da cikakken ikon da zai rika zabar wa kasarnan shugabanni. Ya ce; nasarar Buhari a zaben da ya gabata ya karyata Obasanjon.

Akiolu ya ce dama shi ya yi imanin cewa Buhari shi zai yi nasarar lashe zaben, kuma ya ji dadin da ya zama tsohon shugaban kasar ya ji kunya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!