Connect with us

KASUWANCI

Zai Wuya A Kawo Karshen Cunkoson Manyan Motoci A Apapa – Hadiza Bala

Published

on

Manajin Daraktar Hukumar tashoshin jiragen ruwa ta kasa NPA, Hadiza Bala Usman cunkoson layin manyan motoci a  Apapa, zaiyi wuya ya ragu in har hukumomin da abin ya shafa basu ba’a yi kokarin da ya dace ba ta hanyar kebewa manyan motocin wajen ajiye su.

Hadiza ta sanar da hakan ne a shirin  hirarar shirin gidan Radiyo da akayi da ita a jihar Legas a ranar Litinin data gabata.

Hadiza ta nuna rashin jin dadin ta akan jinkirin da aka samu na kaddamar da garejin ajiye manyan motoci na   Tin Can Island a cikin shekaru goma da suka gabata bayan da Ma’aikatar.

Ayyuka, Wutar Lantarki da Gidaje  ta dauki ragamar gudanar da aikin.

Acewar Hadiza,“Ina son yin amafani da wannan damar don yin kira ga Ma’aikatar Wuta, Gidaje da kuma Ayyukan data gaggauta kammala  garejin na tirelolin na Tin Can Island.”

Ta sanar da cewa, akwai garejin tireloli da Ma’aikatar take ginawa yau sama da shekara goma, na kuma tattauna da Ma’aiakatar tun lokacin dana fara aiki a hukumar NPA yau kusan sekara biyu da rabi kenan na kuma bukaci dasu mikawa hukumata aikin garejin don mu kammala aikin amma har yau bata bayar da damar ba.

Manajin Daraktar Hukumar ta NPA Hadiza Bala Usman ya jadda da cewa, matsalar cunkoson ta tirelolin a   Apapa zai yi wuya a kawo karshen ta, in har ba’a yi kokarin samarwa da tirelolin gareji ba.

A cewar Manajin Daraktar ta  NPA ta yi nuni da cewa, giggina gareji da dama daga wajen tashar    ta jiragen ruwa, zasu taimaka matuka wajen rage cunkoson a tashar ta jiragen ruwa dake jihar Legas.

Ta sanar da cewa, cunkoson ya jima a Apapa   Manajin Daraktar Hadiza Bala Usman ta sanar da cewa, tashar a cikin sati uku da suka wuce, ta janye jinginar data baiwa kamfanin Lilypond na mayar da garejin ajiye tireloli.

Acewar Manajin Daraktar Hadiza Bala Usman,”Ina son inyi kira ga ga gwamnaticin jihohin Legas da  Ogun dasu yi dubi akan bayar da fili don samar da garejin ajiye tireloli a bayan tashar ta jiragen ruwa.

Ta jadda da cewar, “ Dole ne mu kasance muna da garejin na ajiye tirelolin    yadda zamu iya magance cunkoson a Apapa.”

Ta kara da cewa, bazai yuwu ace tirelolin basu da gare ba, domin ko jihohi da kananan hukumomin dake kasar nan, suna samar da gareji ga tireloli.

Hadiza Bala Usman ta yi nuni da cewa, wannan babban kalubale ne kuma zamu ci gaba da yin kokari wajen yin abinda ya dace don kawo karshen dunkoson.   

Manajin Daraktar Hadiza Bala Usman ta kuma koka akan rashin samar na’urorin

Tantance kaya masu aiki sosai a tashar  ta jiragen ruwa, inda ta yi nuni da cewa, hakan yana janyo babban jinkiri na tantance kayan da tura su.

A cewar Manajin Daraktar Hadiza Bala Usman,“ daya daga cikin damur da muke da ita, kayan da ake saukewa a tashar, a zahirance muke tantance su saboda karancin na’urorin tantance kayan a tashar kuma hukumar kwstam, bata kawo na’urorin tantancewa da ake bukata ba, wannan yana daya daga cikin kalubalen da muke fuskanta a hukumar ta NPA.

Manajin Daraktar Hadiza Bala Usman, ta yi nuni da cewa, babu wata hukuma da zata iya dakatar da ko wanne kaya idan har an tantance kayan a cikin tashar ta jirgkn ruwa, amma munga jami’an kwastam, suna hakikancewa sai sun sake tantance kayan da aka riga aka tantance a cikin tashar.

A cewarta, wadannan sune wasu daga cikin kalubalen da muke fuskanta a kokarin mu na samar da sauki wajen yin kasuwanci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!