Connect with us

KASUWANCI

Hukumar SON Za Ta Sa Kafar Wando Daya Da Masana’antun Da Ke Sarrafa Kaya Marasa Inganci

Published

on

Darakta Janar ta Hukumar kula da ingancin abinci ta kasa SON, Barista Osita Aboloma ta sanar da ta yi kurarin cewar, dokar Hukumar tata ta SON ta shekarar 2015, kwakwararan hukunci a yanzj yana jiran masu sarrafa kaya marasa inganci a cikin kasar nan.

Barista Osita Aboloma, ta yi wannan kurarin ne bayan biyo bayan nuna damauwa da Jami’in Hukumar ta SON dake a jihar Ekiti Ayeni Feyisayo saboda yin asarar rayuka da kuma kaya na biliyoyin naira, inda hakan yake kara janyo zubar da mutuncin Nijeriya saboda sarrafa kaya marasa inganci da wasu masana’antu a cikin kassr nan suke yi.

Daraktar Hukumar ta SON Barista Osita Aboloma da kuma Jami’in na Hukumar ta SON dake a jihar Ekiti Ayeni Feyisao sun bayyana hakan ne a jawaban su a garin Sagamu dske cikin jihar Ogun a taron kwana daya na fadakarwa akan sarrafa kayan masana’antu marasa inganci na shiyyar Kudu maso Gabs.

Jami’in na Hukumar ta SON dake a jihar Ekiti Ayeni Feyisaowanda ya wakilci Jami’in gudanar da ayyuka na Hukumar ta SON na shiyyar Kudu maso Gabas Uwargida Tosan Akin-Akosile, ta shedwa mahalarta taron cewar, ba kamar a baya ba, inda duk wani mai sarrafa kaya a masana’antun kasar nanda idan akan kama shi yana sarrafa kaya marasa inganci za’a iya cinsa tarar naira miliyan 20 ko kuma a tasa keyarsa zuwa gidan kaso ba.

Daraktar Hukumar ta SON Barista Osita Aboloma ta dora laifin akan yadda yanayin iyakokin kasar na suke saka-saka, inda hakan ya janyo ake shigo da kaya ba ‘a bisa ka’ida ba.

A cewar Daraktar Hukumar ta SON Barista Osita Aboloma, idan ka sarrafa abu maras inganci tabbas zai kasance maras inganci.

Daraktar Hukumar ta SON Barista Osita Aboloma ta yi nuni da cewar, abinda mutane sukafi so shine kaya masu inganci ds aka sarrafa

Shi kuwa Jami’in na Hukumar ta SON dake a jihar Ogun Injiniya Onipede Olanrewaju ya sanar da cewar, ana shi wayar da kan masu sarrafa kaya dake a cikin jihar akan dokar Hukumar ta SON ta shekarar 2015 wadda ta fayyace which hukuncin da aka da aka tanada, inda hakan yana daya daga yunkurin da akeyi na kawo karshen sarrafa kaya marasa inganci a cikin kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: