Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Sauya Sunan Filin Wasa Na Kasa Zuwa Abiola

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Laraba a birnin tarayya Abuja ya ayyana sauya sunan filin wasa na kasa zuwa sunan Marigayi Moshood Abiola wanda ake ganin shi ne ya lashe zaben 12 ga watan Yunin 1993.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin taron ranar dimokradiyya da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

A lokacin da yake raye, Abiola ya bunkasa harkokin wasanni a Nijeriya da ma Afrika baki daya, inda aka karrama shi a matsayin wani jigo akan harkokin wasanni a Afrika.

Ya kara kungiyar ‘Abiola Babes Football Club,’ dake garin Abeokuta kuma kungiyuar kwallon kafar tana daya daga cikin kungiyoyin da suka yi tashe a kasarnan daga 1982 zuwa 2001. Buhari ya bayyana cewa an yi rashin adalci ga wanda ya lashe zaben 1993, inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsu za su gyara dukkanin wani rashin adalci da aka yi a cikin al’ummarnan. A cewar shugaba Buhari, gyara duk wani rashin adalci, yana daya daga cikin jigon tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a kasarnan. Buhari ya ce daga yau za a rika kiran filin wasa na kasa da suna ‘Moshood Abiola National Stadium.’ Kuma ya tabbatar da cewa; ya maishe da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokradiyya, kuma ya karrama Cif M.K.O. Abiola da Babagana Kingibe da karramawa ta kasa kamar yadda ya yiwa Marigayi Gani Fawehinmi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!