Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Buhari Ta Sha Alwashin Fitar Da ‘Yan Najeriya Miliyan 100 Daga Talauci

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta fitar da ‘yan kasar miliyan 100 daga cikin kangin talauci. Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar jawabin kaddamar da bikin ranar dimokradiyyar iajeriya ta 12 ga watan Yuni a birnin Abuja.

Buhari ya ce, gwamnatin APC za ta jajirce wajen cimma burin magance wa ‘yan kasar akalla miliyan 100 talauci cikin shekara 10 masu zuwa. Shugaban kasa ya kara da cewa yanzu haka, adadin kudaden kasar da ke asusun ajiyarta na kasashen ketare ya karu zuwa Dala biliyan 45.

Alkawarin gwamnatin APC na zuwa ne, kwanaki kadan bayan da wani rahoton hadin gwiwar Bankin Duniya da Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF da kuma Majalisar Dinkin Duniya, ya ce mutane miliyan 91 ke fama da matsanancin talauci a Nijeriya.

Kididdigar ta kara da hasashen cewa, a kowane minti daya, akwai ‘yan Nijeriya akalla 6 da suke afkawa cikin bala’in talauci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!