Connect with us

Uncategorized

Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum Shida Tare Da Jikkata 15 A Jihar Sakkwato

Published

on

A ranar Litinin ne hukumar kiyaye hadararruka ta Jihar Sakkwato ta tabbatar da mutuwar mutum 6 tare raunata mutum15, a wani hatsarin mota wanda ya faru a cikin garin Sakkwato ranar Lahadi. Kwamandar kiyaye hadararuka ta Jihar Sakkwato, Mista Muhammad Kaugama-Kabo ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a garin Sakkwato cewa, hatsarin ya rutsa da wata karamar tirela mai lamba kamar haka JEG 664 DA. Kaugama-Kabo ya kara da cewa, motar mai dauke da mutane da kuma kayayyaki ta yi hatsari ne a kan babbar hanyar Sakkwato zuwa Birnin Kebbi kusa da wani gidan mai mai suna Ada da ke kan hanyar a yankin.

“Hatsarin ya rutsa ne kawai da karamar tirelan, hakan kuma ya faru ne sakamakon mummunar gudu da direban ya ke yi. “Ya na kan hanyarsa ta zuwa garin Illela cikin karamar hukumar Jihar Sakkwato daga Ibadan. “Nan take mutum 6 maza su ka mutu, yayin dea mutum 15 su ka samu mummunar raunika,” in ji kwamandar hukumar kiyaye hadararruku.

Ya ce, tawagar ‘yan sanda sun garzaya da wadanda su ka jikkata zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodio. Kaugama-Kabo ya shawarci masu motoci da su daina tafiya a cikin dare da kuma mummunar gudu wanda zai kai ga salwantar rayukan mutune sakamakon tukin ganga. Ya bukaci mutane wadanda su ka san ‘yan uwansu sun yi ta fiya, da su duba asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo, ko su na cikin wanda hatsarin ya rutsa da su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!