Connect with us

KIWON LAFIYA

Kungiyar Kwararru A Kan Cututtukan Da Su Ka Shafi Fata Ta Ja Kunnen Mutane

Published

on

Kungiyar kwararru na bangaren cututtukan da suke shafi fata ta Nijeriya, sun ja kunnen al’umma cewar idan ana amfani da man fata wanda aka hada, aka kuma fi sani da “organic creams”, hakan zai iya samar da babbar matsala fiye da jin dadin ko kuma wani gyara ita fatar da ake tsammanin ana yinn hakan ne.

Kwararrun sun yi wannan jan kunnen ne wajen wayarc da kan mutane cikin kasuwar Bodija ranar Asabar dindata gabata a Ibadan.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya su Likitocin sun yanke shawarar yin hakan ne, shi al’amarin wayar da kan al’umma, saboda bikin ranar lafiyar fata ta duniya na shekarar 2019 wanda kuma aka yi ma taken “Lafiyar fata da kuma karewar rana”.

Kwararra wadeda ta shahara akan cututtukan da suka shafi fata Ngozi Akueme, ta bayyana cewar, yawancin nau’oin man da ake amfani dasu, wadanda ake amfani dasu saboda a kara kyan fata, sun kunshiu wasu sinadaran da suka hada da steroid da kuma hydrokuinone wadanda kuma a gaba cutarwa za su yi..

Ta cigaba da bayanin cewar “ Da akwai wasun mutane da yawa wadanda suke amfanida damar tasu ta kasuwanci na shi man da kuma yadda suke hada su,sai kuma yadda suke amfani da wata dabara wajen sake mashi marfi, ba kuma su kira shi da suna man da yake canza fata, amma sai suna man da yake sa fata tayi fari da kuma haske.

“Sai su fada maka sun hada sinadaran gyara fatar ne duk da farko sun yi amfani ne da abubuwan gargajiya, amma kuma maganar gaskiya, kayayyakin nasu sun kunshi8 wasu sinadarai, da suka kunshi steroids, hydrokuinone da kuma mercury masu karfin gaske .

“Alal misali shi hydrokuinone idan ana maganar nau’oin man gyara fata ne, bai kamata ace  sun wuce  fiye da kashi  biyu ba,amma kuma wani abinda zai daureb ma mutane kai shine sun kunshin kashi 13 a kasuwannin Nijeriya .

“Ana dai cigaba da yin bincike saboda a samu gano daga cikin nau’oin man ko wanne abinda ya kunsa, nan gaba bada dadewa ba, zamu bayyana shi sakamakon binciken namu, da kuma su hujjojin namu saboda mu kare kanmu kamar dai yadda tayi bayani. ,”.

Ms Akueme wadda take aiki a asibitin kwalejin jami’ar Ibadan ta bayyana cewar shi kokarin shafa nau’oin mai saboda canza kalar fata, ko abinda aka fi sani da, nau’oin man da ke sa fata tayi haske da kuma fari, abin yana kasancewa da wata matsalar gaske wat5akila ma ta hada da da kansar fata, sai kuma bushewa ko kuma kancewar fata, ga kuma cutar ciwon sikari, matsalar dayta shafi Koda, sai kuma uwa uba wanda za a iya haduwa matsalar jaririn da ba a ma kai ga haihuwar shi ba.

Kamar dai yadda ta karabayar da haske shi amfani da man da zai canza fata, yana lalata ita fatar da ake kira Melanin, wadda kuma ita ce take kare fatar jiki daga matsalolin da suka shafi rana.

“Koda yake dai bamu ganin matsalar kansar fata a cikin asibiti, saim kiuma gas hi abin yana neman ya kasance ruwan dare game duniya, kuma duk dalilan da ake bayarwa basu wuce na yadda wasu mata bke ta kokarin canza fatar jikinsu daga baka zuwa fara.

“A ko wacce rana muna tsintar kanmu cikin matsalolin da suka shafi canza fatar jiki, saboda muna ganin misalai wajen wasu marasa lafiya, da suke zuwa da maganganun da basu da dadin ji.

“Kokarin canza launin fata wajen shafe – shafen mai yana samar da matsala wajen warkewar rauni ko kuma cutar data shafi fatar jiki, sai kuma bushewar da kuma kankancewar ita fatar. Shi yasa Likitoci masu tiyata suke fama da matsalar wadanda suke amfani da man canza launin fatar jiki, kamar dai yadda ta yi bayani. ”.

Don haka ma tayi kira da masu ruwa da tsaki a al’amarin cewar su dauki tsattsauran mataki, akan yadda ake kulawa da ake kokarin canza fatar jiki, saboda su nau’oin man sun kasance masu samar da matsala ga al’umma”.

Aderonke Edun wanda shima mamba ne na kungiyar ya ba mutane shawarar su guyji fita waje lokacin da ake rana, wato su wadanda bsuke amfani da su nau’oin man na canza launin fara jiki, ko kuma su rika sa kayayyaki masu kare su da kuma Tabarau na rana.

“Faatar jiki wata abu ce da tak da muhimmanci ga al’ummaita kuma ce babba, bangare na jiki wanda yake da muhimmanci, saboda haka ya dace mu dauki mnatakin daya dace saboda kare ta.

“Mutum yana iya kare kanshi daga matsalar da zai iya fuskanta, amma shi wanda yake amfani da nau’oin man, wajen kada ya fita lokacin da rana take ganiyarta, daga karfe goma na shafe da kuma uku na rana .

“Idan kuma mutum ya fita da rana sai yasa wata Hula wadda zata kare kan shi daga rana, ko kuma ya tsaya a karkashin inuwa, ko kuma amfani da Lema sai kuma shan ruwa mai yawa, saboda jiki ya kasance cikin damshi da kuma ni’ima.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!