Connect with us

KIWON LAFIYA

Mece Ce Majina?

Published

on

Majina wata abu ce wadda ta kan iya bata rai amma kuma lokacin da mutum ba shi da lafiya yana bukatar ta, saboda jikinshi yana bukatar haka domin ya kasance cikin koshin lafiya.

Mucus ko kuma majina wadda aka fi sani da sputum wata abu ce mai santsi santsi, wadda kuma take a Huhu, makogwaro, Baki, Hanci da kuma shi karan Hancin.

Akwai wani sinadarin wanda yake yin majina cikin Hanci da kuma sinuses ko kuma abinda aka fi sani da suna mucous membranes.

Mucus Da Phlegm:

Haka nan ma za ka ji ana ambatar kalmar “mucus” da kuma “phlegm” amma kuma wani abu ita phlegm ita Majina ce wadda kuma ta bambanta da mucus wadda ita ma din majina ce.

Phlegm ita majina ce wadda kuma Huhu biyu da kuma wasu kwayoyin halitta da suke taka rawar gani wajen shakar iska da kuma fitar da ita.

Shi jikinmutum ko wanne lokaci yana samar da majinha, amma kuma mutum yana iya lura cewar da akwai abinda yake faruwa, a sanadiyar wat rashin lafiya, wato kamar Mura, ko kuma wasu sauran cututta.

Wani abu kuma wanda yake da ban mamaki shine idan mutum yana shan Taba sai kasance yana da majina da yawa, shi dai al’amarin yake sa ana samun majina ba wani abinda zai tayar da hankali bane, da kuma akwai dalilai masu yawa wadanda suka sa abin yake kasancewa hakan, koda kuwa ace mutum yana lafiyalau ba tare da wata matsala ba wadda ta shafi rashin lafiya.

Wato kamar ta na yin aiki na kare wasu kwayoyin halitta wadanda suke cikin Huhun mutum biyu, da kuma Makoshi ko kuma Makogwaro, sai kuma Hanci da kuma su kofofin Hancin, inda tana wuraren sun kasance a bushe ko kuma su bushe.

Haka nan ma tana yin aikina na rike wani abinda ba a yarda da shi ba, kamar kwayoyin cuta, wato kamar Kura da dai sauramn makamantansu, inda kuma take hana su wajenn yadda za su watsu cikin jiki daganan kuma su sa mutum ya shiga cikin yanayin rashin lafiya.

Majina ma ta kunshi wasu kwayoyin halitta da kuma enzymes, wadanda su kuma wasu sinadarai ne wadanda ake samun su cikin wasu kwayoyin halitta da suke narka abinci , bayan haka kuma suna wasui sina daran da za su iya kasancewa matsala ga jiki.

Majina Lokacin Da Mutum Bai Da Lafiya:

Bincike ya nuna cewar jikin mutum yana  samar da lita daya da rabi ko wacce rana ta Majina, wannan ma ya  hada har da ranar ma da bashi da lafiya.

Yawancin ita wannan majina tana taruwa ne kasan makogwaro, idan kuma mutum bashi da lafiya, ba dole bane jikin shi ya rika samar da Majina, nkamar yadda ya dace ba wato mai yawa. Amma kuma lokacin da baka da lafiya zaka iya lura da cewar, ko kuma kana jin wani, ko kuma ka nlura cewar ita ko kuma shi nau’in da ka saba gani na Majina ya canza.

Su kwayoyin cuta ko kuma allergens wadanda su kuma wasu kwayoyin halitta ne masu sa aga  wani abu ba kamar yadda aka saba ganin shi ba, hakan yana iya sa samar da ita Majinar da yawa, amma kuma shi wani abu shine ita majinar da ta kasance cikin irin wannan halin, ta kunshi wani sinadarin da ake kira histamine.

Shi sinadarin Histamine shine yake sa kofofin Hanci su kumbura,hakan ne kuma zai sa su rika samar da nau’in Majina, wanda yake ruwa- ruwa, wannan kuma shi ke sa Majina waddabata da kauri tayi ta zuba daga cikin Hanci, tare kuma da yawan yin Hamma, sai kuma ciwo da kuma yadda cikin Hancin yake kamar ya toshe.

Majinar ta mutum ta kan kasance ba wata mai kauri ba ko kuma mai wani danko- danko, lokacin da baka da lafiya, wannan ke nan ya nuna abin yana da wuya ta kasance a kasan makogwaro. Maimakon haka ma sai ta tsaya a Huhunka da kuma makogwaro, wannan shi ke sa, Hanci ya cushe wanda daga karshe ana iya samun matsala wajen yin numfashi ko kuma hadiyar wani abu.

Idan mkutum yana samun Majina wadda bata da kauri wannan yana iya nuna cewar kamar ana samar da karin ita Majina mai yawa, wannan kuma yana iya samar da matsala, kamar yadda Hancin ka zai rika zubzr da Majina mai ruwa- ruwa.

Ita Majina wadda take da kauri wannan alama ce wadda take nuna cikin Hancin ka  a bushe yake ko kuma ya bushe. Wannan kuma yana la’akari ne da irin wurin da ka kasance musamman ma wanda yake busasshe ne, ko dai a sanadiyar zafi ko kuma na’urar sanyaya daki. Ko kuma ba a sha ruwan daya kamata a sha ba, ko kuma sauran abubuwan da ake sha.

Shan kayayyakin sha kamar su Kofi, Shayi, ko kuma Giya wadannan duk su kan yi sanadiyar rasa ruwa.

Amfani Da Wadansu Magaunguna:

Idan kana ganin kana da wadansu ‘yan matsaloli ko dai kana fama matsalar sanyi, ko kuma cutar data shafi wuraren da kake amfanib dasu wajen sha ka da kuma fitar da iskar data kammala amfani a jikin ka. Likitan ka zai iya gwadawa da kuma yawan Majinarka, yadda take, sai kuma irin nau’in da take, wannan fa sai lokacin da yake bincikarka, da kuma sani wane irin magani , ya kamata kayi amfrani da shi.

Nau’in Majina:

Sannu a hyankali zaka iya lura da cewar shi nau’i na  Majinarka ko kuma nace kala abin yana canzawa, musamman lokacin da baka da lafiya,. ko kuma kana fuskantar wasu matsaloli can daban.

Mafi akasari ita Majina kar take bata da wani abinda zai sa nau’inta ya wuce wanda kowa yafi sani, amma kuma lokacin da mutum ya kasance baya da lafiya, Majinar shi ta kan kasance mai ruwan tsanwa, ko kuma wani nau’in da zai yi wuyar ganewa. Wato kodai ta kasance ruwan dorawa mai haske da dai sauransu kamar beige wato shiga wata matsala daban wadda ta shafi lafiya.

Idan kana fama da cutar data shafi sanyin jikinka yana samar da  white bloodcells ko kuma wani jini mai ruwa- ruwa, inda kuma yake aikawa dasu hanyoyi ko kuma kafofin da iska yake shiga, da fita wajen yaki da cututtuka.

Shi white blood cells wanda idan mutum ya samu rauni bayan shi jan jinin ya gama zuba, daga baya kuma sai shi ya biyo baya, ya kunshi wani sinadari, wanda ake kira  neutrophils,wanda kuma shine yake ba Majina nau’in kala mai ruwan dorowa ko kuma ruwan tsanwa.

Hakanan ma Majina ta kan kasance ruwan tsanwa amma lokacin da bata da kauri.

Bugu da kari kuma mutum zai iya ganin nau’in ja ko kuma ruwan kasa- kasa, wannan kuma sai lokacin da mutum ya fyace hancin shi, wannan yana nuna ke nan da akwai jini cikin Majinar shi wanda ya fyace Hancin.

Idan kuma ya kasance da akwai jini cikin Majina wannan yana nuna ke nan da akwai bushewar wasu sinadarai ta kofofin Hanci, ba wani abu bane na damuwa sai dai kawai yawan fyace Hancin da mutum yake yi, shi ya kawo hakan.

Jini dan kadan cikin Majina ba wani abu bane har da zai damu wanda abin ya shafa, amma kuma idan jinin yana zuba ne sosai, da akwai bukatar a samu ganin Likita.Wannan yana nuna  da akwai wata cuta ce mai tsanani  kamar  bronchitis ko kuma ciwon mashako, mutanen da suke fama da wannan cuta su kan yi tarin Majina wadda take da kauri

Hanyoyin Da Za A Fuskanci Matsalar Majina:

Da akwai hanyoyi masu yawa wadanda za ayi magaknin matsalar Majina, da suka hada da wadannan magungunan.

Masu rage ita Majina anan kuma ana iya amfani da (OTC)  ta kofofin Hanci  ake sa shi maganin saboda a rage yawan Majinar dake cikin Huhu, ko kuma su kofofin Hanci.

Su wadannan magungunan suna gyaran Majinar da take mai kauri, amma kuma kada ya kasance an yi amfani dasu fiye da kima,saboda kuwa ana iya haduwa da wata matsala.

Su magungunan suna yin aiki ne wajen dakushe su hanyoyin jinin wadanda suke cikin Hanci, suna kuma kawo cikas wajen rage yawan jinin da yake fita da kuma rage yawan Majinar da take samuwa a wurin.

Idan aka yi aiki da su magungunan wanda kuma har ya wuce kima zai iya sa ita Majinar ta bushe,  zai kuma iya sa ta yi kauri, abindsa kuima shi zai iya kawo ta taru da yawa.

Su magungunan an alakanta su da samar da matsala, watom kamar mutum ya ji jiri yana daukar shi, ya kuma ji jikin shi duk ya mutu bai kuma da wani kuzari, sai kuma hawan jini.

Antihistamines shi wadannan magungunan an yi sune saboda su toshe hanyar, ko kuma su kawo ko kuma samar da rashin aiki sosai na sinadarin histamine, wanda kuma shi wani abu ne a jikin mutum wanda ake samar dashi lokacin da aka samu aukuwar wani bakon abu wanda kuma zai iya cutarwa.

Antihistamines su manyan magunguna ne saboda su yi magani wasu alamomin kamar Hancin da zai rika yin kaikayi, ko kuma Majina ta rika zuba, amma kumsa suna iya samar da wata matsala, kamar a rika jin ana son yin barci ko kuma gajiya, da kuma rashin gane abinda ke mai jin dadi, ko kuma shi Baki ya bushe ko kuma ciwon kai musamnman ma idan an yi amfani da maganin ya wuce kima.

Su yawancin magungunan na matsalolin da ake fuskanta asanadiyar cutar sanyi, wadanda suka hada da OTC, hakika sun kunshi, magungunan wadanda kuma sa Majina ta tsinke, hakan kuma zai sa a samu saukin yadda jiki zai iiya da ita.

Guaifenesin shi wani misali ne na cikin magungunan da aka sab yin amfani da su.

Ita matsalar data shafi Hanci wannan kuma ana bin hanyar data shafi gargajiya ne, wato yadda za ayi maganin matsalar ta Majina, ana kuma miya yin amfani da neti pot, a bulb syringe, ko kuma kwalba wadda aka sa mata ruwa.

Duk wadannan ana iya yin aiki dasu ta hanyar sa ruwan gishiri cikin Hanci, za a rika tura wa ne ta kofofin Hanci biyu, saboda   abin ya narkar da Majinar, yasa ta fito waje.

Cibiyar hana yaduwar cututtuka da maganin suta bayar da shawarar cewar ayiu amfani da wani ruwan magani ko kuma tafasasshen ruwa, lokacin da za ayi aiki saboda rage Majinar wajen narkar da ita.

Lokacin da ake duk ake yiin amfani da duk magungunan wajen bin  hanyoyin da suka kamata, duk da hakan ana fa iya samun matsala, idan shi al’amarin na ragewar wajen amfani da su maguungunan ya wuce kima.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!