Connect with us

MAKALAR YAU

Garin Tunkaho Da Jahilci

Published

on

Taken Kano shi ne “Tumbin giwa ko da me ka zo an fi ka” amma alal hakika, idan mu ka kalli yadda Kanawa su ka zama sannan da yadda al’amura ke ta tabarbarewa a jihar Kano tun daga dawowar siyasa a 1999, za mu fahimci cewa sannu a hankali Kano na koma wa gari da a ke tunkaho da jahilci ne a yanzu. Domin mutanenta, manya da kanana, sun kasa gane cewa su na tunkaho da bazar magabata ne kawai kuma sun kasa bin sawunsu.

Idan na tuna lokacin da muke tasowa, Kano ta kasance gari da ba kanawa kadai ke alfahari da shi ba har ma sauran jihohin arewa. A karshen shekarun 1980’s na halarci kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Bauchi kuma ba zan manta da yadda a duk lokacin da abokina ke gabatar da ni ga wasu abokai a matsayin Ali Kano, zan ga karsashinsu na zama abokaina da kuma irin kallo na girmamawa da su ke min da sha’awa da na ke ba su. Duk inda na sa kafa a arewacin Nigeria ina samun irin wannan girmamawa saboda kawai ni dan Kano ne kuma ana girmama ta. Ban gane dalilin wannan daraja ta Kano sosai a lokacin ba, domin na dauka saboda kawai kasancewarta cibiyar cinikayya ce. Duk da cewa hakan na cikin dalilan, amma daga baya na gano ainihin dalilin. Kano na waje guda sai wanda ya zo in da ta ke zai ganta, amma kanawa na yawo a kowanne lungu da sako na duniya, kuma an sami daidaikunsu,kama daga shugabanni da talakawanta, wadanda su ka yi shura a rikon gaskiya da fadarta tare da kare ta. Kadan daga cikin fitattu, mun ga yadda tarihi ya kawo mana irinsu Muhammadu Rumfa, Ibrahim Dabo, Sarki Alu, Abdullahi Bayero, Aminu Kano, Danmasanin Kano, Mudi Sipikin, Abubakar Rimi, Sabo Bakin Zuwo, Dr Bala Usman, Shehu Umar Abdullahi da sauransu.

Abubakar Rimi ya yi shura wajen jaruntar kanawa ta fadar gaskiya da kare ta, domin a lokacin mulkin Abacha an nada shi ministan sadarwa. A lokacin akwai wani permanent sakatare a ma’aikatar da kowa ke tsoro saboda an ce matsafi ne kuma hatta ministoci tsoronsa su ke. Abubakar Rimi ya sami labarin irn yadda wannan mutum ke cin karensa ba babbaka a ma’aikatar saboda haka ranar da zai kama aiki sai ya isa ofishinsa da sassafe ya ce a kira masa wannan mutum. Ma’aikata su ka ce ai ba ya shigowa ofis da wuri. Nan ta ke Rimi ya sa a ka siyo masa sarka da kwado ya tafi ofishin mutumin ya garkame shi tare da ba da odar cewa idan ya shigo ya zo ofishinsa. Mutane su ka yi jugum-jugum cikin tararrabin me zai biyo baya saboda ba su taba zaton akwai wanda zai iya haka ba. Da ya iso aka gaya masa sakon minister sai ya tafi a fusace, amma ya na zuwa sai Rimi ya ce a gaya masa ya jira. Bayan  jira na tsawonm lokaci a ka ce ya shiga. Abubakar Rimi ya ce masa ba yadda za’a yi minister na ofis karfe takwas wani ma’aikaci bai zauna a nasa ofishin ba. Don haka daga ranar dole kowa ya kasance a ofis karfe takwas. Ta haka Rimi ya karya duk wani lago da izzar wannan mutum da ya zama gagara badau.

A shekarun 1990, an sami barkewar kwalara a Nigeria lokacin da a ka fara jigilar alhazai zuwa Saudia, wanda ya tilastawa hukumomin Saudiyar dakatar da jigilar. Mahajjata kusan 5000 sun kasance a yashe a filin jirgin saman Kano saboda wannan yanayi. Ma’aikatan diflomasiya sun yi iya kokarinsu na ganin an bar sauran mahajjata isa Saudia saboda sauran yan kwanaki a rufe filayen jiragen kasar. Sarkin Kano Ado Bayero ya shirya cikin gaggawa ya tafi Saudi ya gana da Sarkinsu wanda cikin awa ashirin da hudu Saudia ta janye dokar kuma a ka karasa kwashe mahajjata. Wannan lamari ya nuna irin kimar da Ado ke da itai a duniya, musamman ga wanda ya san kafiya irin ta hukumomin Saudia.

Shehin Malamin Jami’a Shehu Umar Abdullahi wanda a shekarun 1980 ya kasance a sahun su Wole Soyinka da Tai Solarin wajen sukar Babangida. Maradona ya bi irin hanyoyinsa wajen jawo Wole Soyinka ya bashi shugabancin a sabuwar hukumar kare hadurra sannan shi kuma Tai Solarin, wanda ya rayu a cikin gajeren wando tun daga Firamare, sai ga shi an bashi Bankin Al’umma, wanda aka wayi gari ya fara saka dogon wando da kwat. Shi kuwa Shehu Umar Abdullahi, duk da gayyata zuwa Billa da kalallame shi da Babangida ya yi, da kuma yadda wata majiya ta ce da zai tafi an kawo kwalin madara shake da masu gidan rana, wanda ya ki karba tare da watsi da tayin mukamin da aka yi masa, ya sa ya mutu cikin kimarsa sabanin wadancan manyan yarbawa yan gwagwarmaya.

Allah ya albarkaci Kano da ire-iren wadannan mutane wadanda sai a rubuta littafi a kan su, amma an wayi gari yau ba sauran irinsu ko guda, saboda shugabannin da talakawa sun raja’a wajen biyan bukatun kai kawai. Wannan halayya ta fito karara a tsakanin shugabanni na siyasa tun daga 1999 zuwa yanzu. Mun ga yadda shekaru 16 na mulkin Kwankwaso da Shekarau su ka shude ba tare da samun wata dorarriyar hanya ta ci gaba ba, idan ba na aljifan tsirarun shugabanni da yan barandansu ba. Idan mu ka kwatanata da jihar Lagos a daidai wannan lokaci, zamu ga cewa Tinubu shi kadai ya jagoranci dora jihar Lagos a bisa turba, yadda tun da daga Awolowo ba a sami wani shugaba a Nigeria da ya dora mutanensa a saiti kamar shi ba. A jerin mutanensa da ya kafa gwamnati a 1999 kuma ya cicciba zuwa gaba sun hada da Yemi Osinbajo (Mataimakin shugaban kasa), Babatunde Fashola (Gwamna kuma Minista), Babatunde Fowler (FIRS), Rauf Aregbesola (Gwamna), Akinwunmi Ambode (Gwamna), Kayode Fayemi (Gwamna, Minista), Musliu Obanikoro (Minista) Gbenga Ashafa (Sanata) Lai Muhammed (Minista), Ibukunle Amosun (Gwamna), Mamora (Sanata) da kuma na kwanan nan wato Kakakin majalisar wakilai, Femi Gabajabiamila. Dukkansu sun yi aiki da Tinubu a matsayin kwamishinoni ko masu bada shawara a 1999, amma a yau su ke rike da Nigeria. Wadannan jajirtattun yan siyasa masu basira sun kai Lagos matsayin da a yanzu ta fi kasashe da yawa a Afirka, kuma sai ka hada jihoji 30 a Nigeria ba za su iya tara abinda ta ke tarawa a wata guda ba. Shin akwai wani kwamishina ko mai bada shawara guda daya na Kwankwaso ko shekarau da ya kai irin wannan matsayi? Shin jihar ta yi wata rawar gani wajen samar da ayyuka ko kudin shiga tsawon wadannan shekaru? Tinubu ya kafa ma’aikata wadda ya kira mai tsare-tsare (Ministry of Strategy) wadda karkashinta su ka debo masu basira daga ciki da wajen Lagos kuma a ka zuba tunanin da ya kawo su matsayin yadda su ke da kuma ikon fada a ji a Nigeria. Gwamna Ambode ya hadu da fushin shugabannin Lagos saboda kaucewa tsarin shekaru ashirin da su ka tsara wanda ya jawo hana shi takara kuma ya hakura ya bi jam’yya.

Malaman sun zama yan siyasa, ba abinda ke gabansu sai kimarsu ta daukaka kuma su cika aljifansu. Ba sa iya gaya wa gwamnati da masu mulki gaskiya, sai dai ma idan masu mulkin sun yi kuskure sai su yi gangami su je gidan gwamnati a matsayin ziyarar goyon baya tare da kalato hadisai su dora mummunar fassara domin goyon bayan shugabanni.

Harkar ilimi da noma an yi watsu da su an maida hankali wajen gina tituna da gadoji domin an maishe su ma’auni na aikin gwamna, yadda har shugaban kasa su ya ke dubawa ya bada makin yabo ga gwamna. Saura watanni shekarau ya sauka ya lura bai yi wani abin a zo a gani ba sai ya kirkiri manyan tituna a birnin Kano, Kwankwaso ya zo ya kama gina azuzuwa da gadoji, sannan Ganduje ya dauka cewa aiki a wajen talaka bai wuce yin gada a birni ba, ba tare da kula da saura sassa da ke kauyuka ba. Kuma an gane cewa ta yin wadannan manyan ayyuka za’a iya kwasar kaso mai tsoka na ladan kwangila.

Su kuwa sarakuna sun gamsu da yadda gwamnati ke kulawa da su wajen mika musu kudaden masarautu su yi yadda su ka ga dama da su. Idan ka ga dama sai ka kashe miliyoyin Naira wajen binne gawa ko biyan kudin internet. Lokacin shekarau ya siyo manyan jeep na Prado wadanda aka rarrabawa hakimai. Da a ka zabi Sunusi Lamido, mun yi murna zaton cewa zai kawo canji a masarautu kasancewar ya na da kwarewa ta hanyoyi da dama kuma ya san abubuwan da ke kawo wa al’umma canji. Maimakon ya tattaro kawunan manyan jihar su kwaikwayi Lagos wajen dora mu kan turba, sai ya gwammace ya yi ta babatu da lasifika ya soki wannan ya soki wancan, abinda ya kai shi cikin tsaka mai wuyar da ya ke ciki a yanzu. Da a baya ya hada kan manya sun samar da dandalin dora  Kano a saiti da Ganduje bai isa ya kawo masa wargi ba saboda ya na da kariya. Ya manta yadda duk da cewa Ambode ne gwamna amma saboda shugabanni ke juya kalar jihar sai ga shi sun hana shi takara balle ya koma kan kujerarsa. Hausawa na cewa “Kowa ya ci shi kadai, to shi kadai zai mutu” wannan Karin Magana ta fada kan Sunusi domin ya tsaya shi kadai ba tare da jan saura ba, yanzu da masifa ta doso shi babu wanda ke taya shi.

A karshe mu sani cewa duk al’ummar da shugabanninta da talakawanta su ka yarda kowa ya yi ta kansa, wallahi wannan al’umma na daf da rugujewa. Idan masifa ta zo kuma kowa sai ta shafe shi. Rashin fadar gaskiya kuma shi ya fi komai jawo wa al’umma asara. Cikakken misali a nan shine yadda Kwankwaso ya kwashi kudin yan fansho ya narka wajen yin rukunin gidajen Amana, Bandirawo da na Kwankwasiyya, wadannan gidaje hakika sun kai gidaje amma kuma saboda ba a yi cikakken shiri ba kuma dama domin wata manufa kawai a ka dosa da su, bayan shekaru biyar gidaje kusan dubu uku sun kasance asara ga gwamnatin Kano. Domin ko haya aka saka a shekaru biyar nawa za’a karba? Sannan a kullum darajarsu sai ja baya ta ke saboda ana ta balle kayayyakin ciki na wasu gidajen. Babban abin takaici shine duk da cewa kwankwaso ya yi wannan kuskure, ina dalilin da Ganduje zai yi watsi da dukiyar talakawa a bar ta ayashe? Na yi imani da cewa da kudadensu su ka zuba wallahi da ba za su bar su haka su na lalacewa ba. Shin tun da kudaden Fansho a ka diba a ka yi aikin, me zai hana a mallakawa ma’aikatan gwamnati da su yan fansho din, su rika biya a sannu-sannu? Ko kuma a nemo hukumar samar da gidaje ta kasa su yi tsarin da ma’aikatan gwamnatin tarayya za su mallaka? Ko kuma a sako bankin bada rancen siyen gidaje na kasa yadda zai din ga baiwa masu ajiya da shi? Saboda kudin talakawa ne sai a barsu su lalace kuma babu wani wanda zai iya gaya wa gwamnati gaskiya? Wallahi Allah ba zai fasa tambayar hakkin mutane a wajen mahukunta ba kuma kowa sai ya yi kididdiga wata rana.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: