Connect with us

RAHOTANNI

Al’ummar Kano Suna Kokawa Kan Rashin Ingancin Ayyukan Kamfanonin Sadarwa

Published

on

Duk da cewa an dan sami aiko da sakon karta kwana mara dalili da kanfononin sadarwa suke wa mutane da suka yi ta kokawa akai har hukumar NCC ta dauki matakin raguwar hakan sai gashi ana kokawa da da tsananin rashin ingancin ayyukan kamfanonin sadarwar wajen biyan bukatun al’umma na wajen kira musamman a yan kwanakinnan a Kano.

Jama’a ne dai da dama keta kukawa da idan sunyi kira basa jin magana kuma koda an dauki kiran nasu suna tsaka da magana sai muryar ta dauke da hakan ke jawo musu matsala.

Sun ce duk da haka kanfanonin sadarwar kan cigaba ne da daukar musu kudi.Wani ma abin takaicin shi ne idan ka kashe ka sake kira sai a hadaka da wanda ka kira din amma baka jin maganarsa baya jin naka amma haka ake cigaba da zare maka kudin kira.

Wani daya koka ya ce, hatta ma sakon karta kwana da ake turawa sai tura, amma ba a aika da sakon ba amma a dauki kudin caji.

Wannan matsalar kuwa ta shafi dukkan kanfononin sadarwan ne dan haka muka yi kokarin tuntubar ofisoshin kanfanonin sadarwar amma ba wani wanda ya iya cewa komai game da korafin.

Munyi kokarin ji daga ofishin hukumar sadarwa na jihar Kano har zuwa wannan lokaci su ma ba mu sami jin ta bakinsu ba game da lamarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: