Connect with us

RAHOTANNI

’Yancin Al’umma Ne Su Gabatar Da Bukatunsu A Kasafin Kudi – Halima Baba

Published

on

Ko bayyana wa masu karatunmu kanki?

Sunana Halima Baba Ahmad Shugaban kungiyar, Center For Jubenile Delinkuency Awareness in Nigeria,(CJDA) ta kasa.

Ga shi kun hada fuskokin masu unguwanni da kungiyoyin fafaren hula yau a nan Bauchi, mene ne makasudin taron da kuka yi?

Allah ya bamu iko mun yi taro na fadakarwa ga al’umma don su fahimci muhimmancin su ‘al’umma’ a cikin batun kasafin kudi wato (Budget), musamman ma da yanzu Allah ya taimakemu shugaban kasa daga sama ya amince akan cewa kowace karamar hukuma za take samun kasonta ne kai tsaye daga lalitar gwamnatin tarayya.

To gaskiya muna da babban aiki a gabanmu, gaskiya muna da matsaloli musamman a kananan hukumomi domin a halin da ake ciki, mutane, kowa ya fi son ya kai kukansa kawai a ba shi kyautar kudi ko don matarsa ta haihu ko hidimar sallah ko wani biki da sauransu, a zahirin gaskiya idan muna son mu ci ribar demokradiyya dole ne sai mun cire batun maula da roko a cikin zukatanmu, mu tashi tsaye mu yi tafiya tare gaba daya wanda zai kaimu ga samun ci gaba a kasa, wannan shine dalilin shirya wannan taron.

Alhamdullahi daman wannan wayar da kan jama’a dangane da batun kasafin kudin mun jima da farawa, amma mun sake kaddamar da shine a jihar Bauchi domin gayar muhimmancinsa a cikin al’umma, muna sa ran ba ma karamar hukumar Bauchi ba, za mu kara zuwa sauran kananan hukumomi idan muka samu taimakon Allah za mu zarce har zuwa shiyyar arewa maso gabas gaba daya.

Takamaimai mene ne kuke son jama’a su fahimta ganin cewar shi kasafin nan wasu ke kebance kansu su tsara ba wai jama’a ke yin sa ba, kuna son jama’an suke kawo nasu ra’ayin ne ko yaya?

Ai daman a dokan kasa batun kasafin kudi gwamnati za ta yi nata amma mu ma al’umma muna da tamu gudunmawar a ciki, domin dokar kasa ne ya ba mu damar cewa mutanen da muke cikin al’umma za mu gabatar da na mu koke da bukatun da muke son su fito mana a cikin kasafin kudi. To a zahirin gaskiya mutanemu ba su fahimci wannan lamarin sosai ba sam, don haka ne mu kuma muka tashi tsaye shiga lunguna da sakona domin fahimtar da jama’a matukar alfahun da ke cikin shiga cikin batun kasafin kudi ke da shi a garemu mu al’umma.

Kowani dan kasa yana da ‘yancin ya fadi kokensa ya rubuta bukatarsa ya dauka ya kai karamar hukumarsa ko kuma ya kai zuwa ofishin tsara kasafi da kudi yake yankinsa domin a samu a sanya a cikin kasafin kudi, wannan aikin ne muka sanya a gabanmu domin ake tafiya tare da al’umma wajen gudanar da gwamnati kamar yadda dokar kasa ya baiwa al’umma wannan ‘yancin.

Mu na son jama’a su fahimci wannan batun na kasafin kudi sosai, don bai dace a ce kuna bukatar abu kaza amma kun gaza isar wa gwamnati shi ba, daga karshe gwamnati kuma ta kawo muku wasu aiyukan da kila da basu ne aka yi ba, da wanda kuke son aka yi da ci gaban yankinku ya fi inda yake, don haka muna son jama’a su bamu hadin kai da har za a samu zarafin ciyar da wannan batun gaba.

A jihar Bauchi kadai kuke wannan buga-bugar ko ya abin ya ke?

Kamar wanda muka yi a da baya wanda ICPC suka bamu muka yi, mun aiwatar ne a shiyyar arewa maso gabas gaba daya. Amma wannan da muke kan gudanarwa, kungiyarmu ce ta ke aiwatarwa, mun kuma tsara cewar mun kaddamar ne a jihar Bauchi a cikin karamar hukumar Bauchi daga bisani kamar yadda na shaida maka da fari za mu fadada wayar da kan jama’an zuwa sauran kananan hukumomin jihar 19, idan kuma muka samu zarafi da cikakken damar da muke nema, za mu yi kokarin aiwatar da wannan shirin a shiyyar arewa maso gabas gaba daya domin matukar alfanun da hakan ke da shi a rayuwarmu.

Ya kika fahimci inda jama’an da suka halarci taron suka amshi kiranku?

Alhamdullahi don kusan kowa ya zo ne da wani kurji ne a zuciyarshi wanda yake kokarin ya fasa don mutane su amfana, musamman matasanmu da su basu gane kan batun kasafin kudi ba, muna rokon Allah ya sa su gane cewar suna da hakki a batun kasafin kudi, domin idan matasanmu suna gane cewar suna da ‘yanci a batun kowa ya mika kokensa, to ina ga maganar a ce babu makaranta ko makarantu sun lalace, ko maganar asibiti ko matasa suna fama da rashin aikin yi duk zai tafi, domin gaskiyar magana ita ce idan aka ce mu al’umma mun bayar da bukatunmu ka ga dole ne idan an zo aiwatar da aikin nan tilas a dibi matasanmu aiki, mu fatanmu da burinmu shine mu ga matasa sun daina zaman banza. Saboda da ko, matasan sune shugabanninmu a nan gaba, amma ba zai iyu ba, dole ne sai sun kwabi kansu, su yi fada wa kawukansu su zama mutane na gari, idan Allah ya taimaka suka zama mutane na gari duk magana ya kare matsalolin ma ba za a samu ba.

Kuna da wani shiri nan gaba na bibiyar shi kasafin da aka tsara an aiwatar da shi ko kuma kawai a zane a takarda zancen ya tsaya?

Ai duk abun da za mu yi muddin ba a aiwatar ba da sauran rina a kaba. Da hadin guiwar masu ruwa da tsaki za mu tabbatar da cimma nasarar bibiya da tabbatar da bukatar da ya shiga cikin kasafi an aiwatar.

Za mu yi bibiya Insha Allahu akwai kwamitin  da muka horar da su daga cikin mahalartanmu, a cikin karamar hukumar nan muna da masu ungunni da masu gundumomi da suke cikin wannan tafiyar kowani bukatu da ke cikin gari sun sanshi, duk wani mai unguwa ko mai gunduma ya san bukatun da ke yankinsa, za mu yi aikin hadaka da masu unguwanni wajen tattara bukatun jama’a muna da wadanda suke ofishinmu aikinsu amsar bukatun jama’a, mu kuma idan muka tattara bukatun jama’a za muke bibiyar sahun abun da jama’a suke bukata. A duk lokacin da muka tabbatar wani aikin da muka shigar ya samu shiga cikin kasafin kudin shekara, za mu hadu da al’umma mu ke bibiyar aikin tun daga farko, kama daga ingancin aikin da za a yi ko ake yi.

A gefe daya kuma muna da masana kan harkar zane-zane wadanda sune za ku sanya mana ido wajen lura mana da ababen da mu bamu sansu a zahirance ba, su kuma suna da kwarewa sosai a kai domin aiki yake inganta, don a zahirin gaskiya idan ma aka samu aiki amma aka samu baida ingaci to an gudu ba a tsara ba, don haka ina tabbatar maka bibiyar aiki sau da kafa tilas ne mu yi da zarar bukatun mu al’umma ya samu shiga cikin kasafi.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: