Connect with us

KASUWANCI

An Samu Asarar Naira Biliyan 111 A Kasuwar Sayar Da Hannun Jari

Published

on

An samu asarar naira biliyan 111 a kasuwar sayar da hannun jari ta kasa NSE a hada-hadar da aka gudanar saboda faduwar farashi na kasuwanci da aka sayar da kaya talatin da daya a kasuar.

Dukkan shiyar da kuma kasuwar an lissafa sun ragu zuwa  kashi 0.88  bisa dari da ya kusa kaiwa  34,110.22 da kuma naira tiriliyan 12.452 baki daya.

Har ila yau, sauran kididdigar ta saboda ran da aka sanya akan mai da kuma iskar Gas harda  ita kasuwar da ake sayar da kayan, inda suka hau zuwa kashi 0.15 bisa dari da kuma kashi 0.38 bisa dari baki daya, inda kuma  kusuwar da kuma ASeM suka kulle ba tare samun komai ba.

Farashin  kaya talatin da daya suka durkushe, inda suka haura samada da ashirin da shida a ranar laraba, inda kuma kaya sha tara suka kare farashinsu.

Kididdigar fanin banki ta sauka da kashi 2.49 bisa dari haka bankin Diamond Bank Plc, Ecobank Transnational Incorporated, Fidelity Bank Plc, Guaranty Trust Bank Plc, da Jaiz Bank Plc duk sunyi asara.

Bugu da kari, fannin Inshora kididdigarsu ragu zuwa kashi 0.21 bisa dari saboda asarar da kamfanin Inshora na AIICO Plc, Law Union and Rock Insurance Plc, Mutual Benefits Assurance Plc, da kuma Niger Insurance Plc su ka yi.

Har ila yau, kayan da masu saye suke saye sun ragu da kashi 1.06 bisa dari.

Kamfanon da suke akan gaba da sukayi kokari sune,AG Lebentis Nigeria Plc, Fidson Healthcare Plc, Sobereign Trust Insurance Plc, Royal Edchange Plc, da Unity Bank Plc,wadanda suka samu riba har ta kashi 10 bisa dari  da kashi  9.09 bisa dari, da kashi 8.70 bisa dari da kashi 8.33 bisa dari da kuma kashi 6.76 bisa dari.

Wadanda kuma suke akan gaba wajen tabka asara sune, kamfanin Inshora na Wapic Plc, Eterna Plc, Law Union and Rock Insurance Plc, Standard Alliance Insurance Plc, da kuma Unileber Nigeria Plc, wanda sukayi asarar kashi 10 9.42 da kshi  9.09 bisa dari da kashi  8.57 bisa dari  da kuma kashi 6.40 bisa dari baki daya.

Jimlar shiya biliyan 1.147 data kai naira biliyan 12.546 da akayi hada-hadar kasuwanci na 16,649 da akayi kasuwancinsu a satin da ya wuce masu zuba jari suka zuba a kasuwar ta shinku sabanin jimlar  shiya ta naira miliyan 925.630 da aka kiyasta ta kai naira biliyan  8.333 da suka shiga hannui a hada-hada 15,565.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!