Connect with us

WASANNI

Har Yanzu Babu Wanda Ya Taya Pogba Da Lukaku, Cewar Solkjaer

Published

on

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa, kawo yanzu babu kungiyar da ta nemesu akan ‘yan wasanninsu guda biyu Paul Pogba ko kuma Rumelu Lukaku wadanda ake kyautata zaton zasu bar United din kafin fara kakar wasa mai zuwa.

Pogba, mai shekara 26 a duniya dai ana dangantashi da barin kungiyar zuwa Jubentus ko kuma Real Madrid bayan da wakilinsa Mino Riola ya bayyana cewa dan wasan yanason barin Manchester United a wannan lokacin.

Shima abokin aikinsa , Rumelu Lukaku, ana ganin zai bar kungiyar bayan da kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta dukufa wajen ganin ta samu damar daukar dan wasan wanda Solkjaer yace yanason cigaba da aiki dashi.

“Akwai labarai kala-kala akan ‘yan wasanmu yayinda wasu ake cewa zasu tafi wasu kuma ake cewa zamu kawo sai dai daman idan kana buga wasa a Manchester United dole sai kayi hakuri da irin wadannan labaran” in ji Solkjaer

Ya cigaba da cewa “ Kawo yanzu dai babu wata kungiya data zo ta samemu akan daya daga cikin ‘yan wasanda ake cewa zasu tafi wato Paul Pogba da Rumelu Lukaku kuma nayi Magana dasu a kwanakin baya akan halin da suke ciki”

Kawo yanzu dai Manchester United tana kasar Australia inda anan take daukar horon wasannin share fage kuma a ranar Asabar United din zata fafata da kungiyar Perth Glory sannan bayan kwana hudu kuma ta sake fafatawa da tsohuwar abokiyar hanyyarta, wato Leeds United.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: